Zamfara: PDP Ta Yaba Wa Kotun Abuja Kan Nasarar Da Ta Samu
[ad_1]
Jam’iyyar PDP reshen Jihar Zamfara ta nuna godiya ga Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan hukuncin da ta yanke a ranar Talata da ta gabata.
Shugaban riƙo na jam’iyyar a jihar, Hassan Daudawa, ya ce nasarar kotun ta ƙarfafa gwiwar magoya bayan jam’iyyar a dukkannin matakai.
- Gwamnatin Tarayya Ta Buɗe Makarantar Koyar Da Harsuna A Kano
- Gwamnatin Tarayya Ta Buɗe Makarantar Koyar Da Harsuna A Kano
Hukuncin kotun ya yi watsi da ƙarar da Samuel Anyanwu ya shigar, wanda ke neman a tabbatar da shi a matsayin sakataren PDP na ƙasa.
Alƙalin kotun, Muhammed Umar, ya ce wa’adin sakataren PDP na ƙasa ya ƙare a watan Disamba 2025.
Daudawa ya ce: “Dole ne mu yi farin ciki da wannan nasara wacce za ta ƙarfafa tsarin jam’iyyarmu kuma ta ba mu damar tsayawa takara a dukkanin muƙamai a babban zaɓen 2027.”
Ya ƙara da cewa dukkanin muƙamai a jam’iyyar, tun daga Kwamitin Aiki na Ƙasa (NWC), Kwamitin Zartarwa (NEC), Kwamitin Amintattu, da Wakilai na Ƙasa, suna nan daram.
Daudawa ya taya hedikwatar PDP ta ƙasa murna tare da tabbatar da biyayya ga Shugaban Jam’iyyar na ƙasa, Kabiru Turaki.
Ya ce nasarar ta karya ƙoƙarin jam’iyyun adawa da kuma waɗanda ke son raba PDP saboda rikici.
A ƙarshe, ya yi kira ga al’ummar Nijeriya da su koma jam’iyyar PDP mai gaskiya da kishin jama’a don ceto al’umma daga ƙangin da APC ta jefa ƙasar.
[ad_2]
Source link