INEC Ta Gyara Jadawalin Zaben 2027 Tare Da Tsawaita Wa’adin Mika Rajistar Jam’iyyun Siyasa
[ad_1]
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da gyara jaddawalin zaben 2027, wanda ya bai wa jam’iyyun siyasa karin lokaci don gabatar da rajistar mambobinsu ga hukumar.
Sanarwar ta biyo bayan taron da aka yi ranar Talata tsakanin hukumar da shugabannin jam’iyyun siyasa, wanda aka bayyana damuwa kan lokacin da za a mika rajistar mambobin jam’iyyun siyasa.
- Gwamna Uba Sani Ya Kulla Yarjejeniyar Naira Biliyan 15 Don Inganta Wutar Lantarki A Kaduna
- Fadar Shugaban Ƙasa Ta Soki Jami’iyyar ADC, Ta Ce Su Fuskanci Matsalolinsu
A cikin wata sanarwa a daren Juma’a, kwamishinan INEC kuma shugaban kwamitin wayar da kan masu zabe, Mohammed Kudu Haruna, ya ce gyaran na nufin daidaita jadawalin da kwanaki 21 da aka tanada a sashe na 77(4) na dokar zabe, 2026, tare da ainihin kwanakin da jam’iyyun siyasa suka kayyade da kansu.
Sakamakon haka, an kara wa’adin karshe na mika rajistar zuwa ranar 10 ga Mayu, 2026, daga ranar 21 ga Afrilu.
A karkashin sabbin ka’idodin, jam’iyyun siyasa suna da ‘yanci su kayyade ranakun zaben fid da gwani a cikin lokacin da aka amince da shi daga 23 ga Afrilu 2026 zuwa 30 ga Mayu 2026.
Duk da haka, hukumar ta jaddada cewa dole ne a mika rajistar mambobin jam’iyyu kafin kwanaki 21 gabanin gudanar da zabukan fitar da gwani.
Ya jaddada muhimmancin wadannan canje-canjen don tabbatar da tsarin zabe mai kyau, yana gargadin cewa ya zama dole jam’iyyun su bi wannan jadawalin don gujewa jinkiri a yayin gudanar da zaben 2027.
[ad_2]
Source link