NPA Ta Kaddamar Da Tsarin Kara Bunkasa Fitar Da Kayan Da Basu Da Nasaba Da Fannin Mai
[ad_1]
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Kasa ta kasa ta kaddamar da cikakken tsari, domin ta kara habaka fannin da bai shafi fitar da man fetur ba.
Hakan na kunshe ne, a cikin sanawar da jaridar Punch ta samu daga gun NPA, a ranar Lahadin da ta gabata.
- CBN Ya Ɗage Tsarin Dijital, Zai Biya Mahajjata Kuɗin Guzurinsu A Hannu
- INEC Ta Gyara Jadawalin Zaben 2027 Tare Da Tsawaita Wa’adin Mika Rajistar Jam’iyyun Siyasa
A cewar sanarwar Shugaban hukumar Dakta Abubakar Dantsoho, ne ya bayyana haka a taro karo na 37 da cibiyar baje koli ta kasuwanci, masana’antu, ma’adanai da kuma aikin noma ta jihar Enugu ta shirya.
Ya ce, NPA na kan kara saita tsarin tafiyar da fannin na sufurin jiragen ruwan kasa, domin a hada masu sarrafa kaya na cikin gida, musamman, domin amfanin kanana da kuma matsakaitan sana’aoi, domin su kai mataki, irin na duniya.
Dantsoho ya zayyano irin mahimmancin da jihar ta Enugu, take da shi, a bangaren hada-hadar kasuwanci, musamman a tsakanin Kudu Maso Gabashin kasa
Ya kara da cewa, yadda tsarin jihar yake, ya kasance akwai dimbin damar da za a iya amfana da ita, wajen fitar da kayan da aka sarrafaa, a cikin kasar, zuwa ketare, musamman kayan da suka sahfi amfanin gona.
Ya kuma yabwa cibiyar, musamman ci gaban da take ci gaba da samarwa wajen bunkasa kasuwanci da kuma gudanar da hada-hadar kasuwanci, ta kasa da kasa.
Ya ci gaba da cewa, a bisa kokarin da ake yi na rage cunkoso a tashoshin jiragen ruwan kasa da kuma kara inganta ayyukan NPA, D antsoho ya bayyana cewa, NPA na kan zuba jari, na gudanar da aikin yin garanbawul a tashoshin jiragen ruwa na Onne, Warri, da kuma na Calabar.
A cewarsa, NPA na kuma ci gaba da taimaka wa, sabbin tashoshin jiragen ruwa na yankuna.
“Gangane da sabunta zuba jari da muka zuba a kan kayan aiki a tashoshin da ke a yankin Gabas, mun samar da ka’ida, na irin kayan da za a yi aiki da su a tashoshin jiragen ruwa, musamman domin a magance, duk wani cunkoson jiragen ruwa, a tashoshin,” Inji Dantsoho.
Ya sanar da cewa, fannin hada-hadar kasuwanci, ya kasance daya daga cikin ginshikan da ke kara habaka tatalin arzikin kasar nan.
Ya kara da cewa, NPA ta himmatu wajen ganin ta kawar da duk wani tsaiko da ke kawo cikasa, wajen fitar da kayan da aka sarrafa, a cikin kasar, musamman domin a kara bayar da damar gudanar da gasa, a bangaren hada-hadar kasuwanci.
A cewarsa, sauye-sauyen da NPA ta kirkiro da su a bangaren fitar da kaya zuwa ketare, an kirkiro da su ne, domin samar da saukin fitar da kayan da aka sarrafa a kasar
“Kamar yadda wasu ke da masaniya kan tsarin da NPA ta kirikiro da shi na EPT, na ci gaba da taimaka wa wajen fitar da kaya zuwa ketare,” A cewar Dantsoho.
Shugaban ya kara da cewa, domin a kara inganta sahihancin ayyukan hukumar da kuma samar da saukin yin kasuwanci, wadanda suka yi daidai da tsarin kasuwanci na gwamnatin tarayya NPA, na ci gaba da wanzar da tsarin NSW na kasa.
“Domin a samun cin yawan dogaro kan ayyukan ‘yan Adam, hukumar ta kara mayar da hankali, wajen yin amfani da tsarin na NSW,” Inji shugaban.
Ya sanar da cewa, a yanzu wannan tsarin na NSW, shi ne ake yin amfani da shi, a fadin duniya, tare da kuma hada masu ruwa da tsaki damar gudanar da hada-hadar kasuwancinsu.
Dantsoho ya kuma bai wa masu ruwan da tsaki da masu zuba jari da kuma masu fitar da kaya zuwa kasar waje, tabbacin cewa, hukumar a shirye take domin ta yi hadaka da su.
Ya kuma yi kira a gare su, da su yi amfani da damar da hukumar ta NPA ta samar domin su kara bunkasa ayyukansu.
”Kofar mu ako da yaushe, a bude take domin yin hadaka, mun kuma samar da matakai domin cimma burin da hukumar, ta sanya a gaba, “ Inji Dantsoho.
[ad_2]
Source link