Gobara ta kone azuzuwa 34 a makarantar kiwon lafiyar dabbobi ta Kano
[ad_1]
Wata gobara da ta tashi ta kone azuzuwa 34 a Makarantar Kiwon Lafiyar Dabbobi da ke Karamar Hukumar Kabo a Jihar Kano.
A cewar Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:53 na ranar Litinin.
Jami’in ya ce ofishin kula da gobara ya samu kiran gaggawa daga wani mai suna Jamilu Abubakar, wanda ya bayar da rahoton tashin gobarar a cikin makarantar.
Ya ce nan da nan aka tura ma’aikatan kashe gobara daga ofishinsu na Rijiyar Zaki zuwa wurin.
“Da suka isa, ma’aikatanmu sun gano ginin bene mai girman kusan kafa 500, wanda ake amfani da shi a matsayin Makarantar Lafiyar Dabbobi, yana ci da wuta,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa azuzuwa 16 sun ƙone kurmus, yayin da wasu 18 suka dan kone kaɗan.
Sai dai an yi nasarar shawo kan gobarar, inda aka hana ta bazuwa zuwa sauran azuzuwa da ofisoshin makarantar.
“An tura motar kashe gobara ɗaya daga ofishin Rijiyar Zaki domin shawo kan lamarin,” in ji jami’in, yana danganta nasarar aikin da saurin amsa da ma’aikatan suka yi.
Babu wanda ya rasa rai a lokacin da ake rubuta wannan rahoto, yayin da ba a kai ga bayyana musabbabin gobarar ba tukuna.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link