AFCON 2025: CAF Ta Ci Tarar Algeria, Ta Dakatar Da Ƴan Wasanta
[ad_1]
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afrika (CAF) ta ɗauki matakai masu tsauri kan ƙasar Algeria da wasu ƴan wasanta bayan rashin ɗa’a da suka nuna a lokacin da kuma bayan wasan daf da na kusa da na ƙarshe na Gasar AFCON 2025 da suka fafata da Nijeriya.
A cikin wata sanarwa da CAF ta fitar a ranar Laraba, ta ce Kwamitin Ladabtarwarta ya zauna domin duba abubuwan da suka faru a wasan da aka buga ranar 10 ga Janairu, 2026, inda ya yanke hukunci da dama.
Daga ciki sun haɗa da Mai tsaron ragar Algeria, Luca Zidane, an dakatar da shi daga buga wasanni biyu na CAF saboda rashin ɗa’a, yayin da mai tsaron baya Rafik Belghali ya samu dakatarwa na wasanni huɗu bisa zargin nuna halin tsokana da tsoratarwa ga alƙalin wasa a ƙarshen wasan, amma wasanni biyu daga ciki an dakatar da aiwatar da su na tsawon shekara guda a matsayin gwaji.
- AFCON 2025: Lookman Da Osimhen Na Daga Cikin Zaratan Yan Wasa 11 Na Bana
- Gwmantin Kaduna Ta Tabbatar Da Sace Masu Ibada 177 A Kajuru
Haka kuma, CAF ta ci hukumar Ƙwallon Ƙafar Algeria (FAF) tarar kuɗi har dala 100,000 bisa halayen ƴan wasa, jami’ai da magoya baya. Tarar ta haɗa da dala 5,000 saboda katunan gargaɗi biyar da ƙungiyar ta samu, da dala 25,000 saboda halayen da suka ɓata martabar wasan a ƙarshen wasa, da dala 5,000 saboda amfani da hayaƙi daga magoya baya, da dala 5,000 saboda jefa abubuwa cikin fili, da dala 10,000 saboda gazawa wajen bin matakan tsaro, da kuma dala 50,000 saboda nuna halaye na cin zarafi ga jami’an wasa.
CAF ta bayyana cewa ba a ɗauki wani mataki kan ƙungiyar Nijeriya ba dangane da lamarin. Rikicin ya ɓarke ne bayan an busa tashi a ƙarshe, yayin da Super Eagles ta tsallake zuwa gaba a tsakiyar zanga-zangar ƴan Algeria da magoya bayansu kan ƙwallayen da ake takaddama a kansu, musamman zargin rashin ba su bugun fanareti.
Bidiyoyi da suka yaɗu a kafafen sada zumunta sun nuna ƴan Algeria na tunkarar alƙalai da yin arangama, yayin da magoya baya ke jefa abubuwa da karya shingayen tsaro. Tarayyar Ƙwallon Ƙafar Algeria ta ce za ta ɗaukaka ƙara, tana kallon hukuncin a matsayin mai tsauri tare da neman a sake duba aikin alkalanci.
[ad_2]
Source link