2027: ’Yan APC kaɗai za a bai wa muƙami idan aka ci zaɓe — Nentawe
[ad_1]
Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce iya masu yi wa jam’iyyar biyayya ne kaɗai za a bai muƙaman siyasa bayan zaɓen 2027.
Ya bayyana haka ne lokacin wani taro da ya gudana a Abuja.
Nentawe ya ce: “Da zarar an ba ka muƙamin siyasa, kai ɗan siyasa ne. Babu wani muƙamin ƙwararru.”
Ya jaddada cewa duk wanda aka naɗa dole ne ya tallafa wa jam’iyyar, ya shiga harkokin siyasa tun daga tushe, kuma ya kare manufofin gwamnati.
“A matsayina na shugaban jam’iyya, zan yi tsayin daka wajen kare wannan matsaya cewa idan ba ka shirya tafiya tare da mu ba, ba za a ba ka muƙami ba,” in ji shi.
Nentawe, ya nuna muhimmancin yankin Arewa Maso Yamma, inda ya ce yankin ya kasance ginshiƙin nasarar APC.
Ya ce da kashi 48 na ’ya’yan jam’iyyar APC daga yankin matasa ne masu shekaru 18 zuwa 35, wanda ke nuna cewa matasa su ne ginshiƙi a tsarin jam’iyyar.
Ya kuma yi gargaɗin cewa waɗanda aka bai wa muƙamai, amma suka guji shiga harkokin siyasa na haifar musu da matsala.
“Dole a kare manufofin gwamnati, a bayyana su, kuma a tallata su ta hannun waɗanda ke aiwatar da su. Masu muƙami ba za su iya ware kansu daga manufofin jam’iyya ba.”
Masana harkokin siyasa sun yi gargaɗin cewa fifita biyayya ga jam’iyya sama da ƙwarewa na iya haifar da naƙaso ga harkar shugabanci.
Abubakar Ibrahim, Malami a Jami’ar Tarayya da ke Lafia, ya ce bai wa iya waɗanda ’yan jam’iyya ne na iya raunana tsarin shugabanci.
Abubakar Ibrahim ya ce: “Naɗa mutanen da ke yi wa jam’iyya biyayya kaɗai tare sa watsi da ƙwarewa na iya rage ƙimar gwamnati a idon jama’a.”
Usman Aliyu Hayatu, masani a Zaria, ya ƙara da cewa wannan tsarin na iya fifita buƙatun ’ya jam’iyya a kan buƙatun ƙasa:
“Duk wanda aka naɗa saboda yi wa jam’iyya kawai zai fi yi wa shugabanninsa hidima a kan gaskiya, bin doka, da adalci a tsarin mulki.”
Dokta Aminu Hayatu daga Jami’ar Bayero ta Kano, ya ce wannan mataki na nuna yadda iko zai tafiyar da jam’iyya kafin zaɓen 2027.
Hakazalika, ya ce hakan zai iya sanya ofisoshin gwamnati su zama wuraren yaƙin zaɓe, lamarin da zai raunana ayyukan gwamnati da amincewar jama’a.
Jam’iyyar PDP, a gefe guda ta ce za ta ɗauki matakai daban-daban domin ganin ta lashe zaɓen 2027.
Sakataren yaɗa labarai na PDP na ƙasa, Ini Ememobong, ya ce: “Idan jam’iyyarmu ta ci zaɓe, za mu gudanar da tsarin da zai haɗa ’yan siyasa da ƙwararrun mutane.
“Abu mafi muhimmanci shi ne abin da wanda aka bai wa muƙami zai bayar, ko ɗan siyasa ne ko ƙwararre.”
Ya ƙara da cewa ƙwarewa za ta zama tushen naɗin muƙamai.
“Shugabanci abu ne mai muhimmanci wanda ba za a bar shi a hannun ’yan siyasa kaɗai ba. Kowa na da rawar da zai taka.”
Masana sun yi gargaɗin cewa idan APC ta aiwatar da wannan mataki, mutanen da ke da ƙwarewa na iya rasa damammaki, wanda hakan zai iya kawo cikas ga ci gaban ministoci da hukumomi, da raunana ingancin cibiyoyin gwamnati.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link