Mutum 4 sun mutu, 5 sun ɓace a kifewar kwale-kwale a Sakkwato
[ad_1]
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta tabbatar da mutuwar fasinjoji huɗu a wani hatsarin kwale-kwale a ƙauyen Kojiyo da ke Ƙaramar hukumar Goronyo.
Lamarin ya faru ne a kogin Rima a Sakkwato lokacin da kwale-kwalen da ke jigilar fasinjojin ya kife da misalin ƙarfe 1:00 na ranar Lahadi.
An sanar da ɓacewar fasinjoji biyar, yayin da aka yi nasarar ceto wasu 41.
An bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawun gwamnan Sakkwato Ahmed Aliyu, Malam Abubakar Bawa a ranar Juma’a.
An tabbatar da hakan ne biyo bayan wani ƙwaƙƙwaran bincike da jami’an Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) da kuma Majalisar Ƙaramar Hukumar Goronyo suka gudanar.
Idan dai za a iya tunawa, jim kaɗan bayan samun labarin faruwar lamarin, tawagar gwamnatin Jihar Sakkwato, ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Idris Muhammed Gobir ya ziyarci yankin ne domin jajantawa al’ummar Ƙaramar Hukumar Goronyo da iyalan waɗanda suka rasu.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link