Kano Pillars Ta Ƙare Zagayen Farko Na Gasar Firimiyar Nijeriya A Jan Layi
[ad_1]
Daga Abba Ibrahim Wada
Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta lallasa Nasarawa United da ci 3-0 a wasan farko da ta buga a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata a birnin Kano bayan kammala Wasannin Gida a filin wasa na Muhammadu Dikko dake birnin Katsina yayin da suke Fuskantar hukuncin da hukumar gasar NPFL ta Nijeriya ta yi mata, wasan kuma shi ne na karshe a zagayen farko na kakar wasan kwallon kafa ta Nijeriya ta shekarar 2025/2026.
A wasan farko da Pillars ta buga a filin wasa na Sani Abacha tun bayan da aka kore su zuwa filin wasa na Muhammadu Dikko a watan Oktoba bayan wani rikici da ya barke a wasansu da 3SC ta Ibadan, Mustapha Umar ne ya fara zura kwallo a minti na 28 kafin zuwa hutun rabin lokaci, bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Chiedozie Okorie ya kara kwallo ta biyu ga Pillars a minti na 68 kafin Mustpaha Jibrin ya tabbatar da nasarar a minti na 72.
- Tawagar Jami’an Kiwon Lafiya Ta Sin Ta Tallafawa Marayu A Saliyo
- Nasiha Ga Masu Kudin Da Ba Sa Fidda Da Zakkah Kuma Ba Sa Taimakon ‘Yan’uwa
Pillars ta samu nasarori uku a waje a jere a Wasannin da suka buga da El-Kanemi Warriors, Katsina United, da Abia Warriors sannan sai nasarori a Bayelsa United, Kun Khalifat, da Plateau United bi da bi, amma kuma duk da haka Pillars ta kammala zagayen farko na gasar a matsayi na 18 da maki 19 a wasanni 19 da suka buga a bana.
[ad_2]
Source link