Adadin Fasinjojin Jiragen Kasa Na Sin Ya Kai Matsayin Koli Sakamakon Kammalar Hutun Bikin Sabuwar Shekara

[ad_1]

Yau Asabar ce ranar karshe a hutun bikin sabuwar shekarar nan ta 2026, wanda hakan ya haifar da karuwar fasinjojin dake bin jiragen kasa a kasar Sin, zuwa adadin koli sakamakon fasinjoji masu komawa wuraren ayyukansu bayan kammala hutun, kamar dai yadda alkaluman kamfanin sufurin jiragen kasa na Sin suka bayyana.

An yi hasashen cewa, adadin jiragen kasa masu sufurin fasinjoji zai kai miliyan 17.45 a yau Asabar, da kuma shirin karin jiragen kasan har 1,343 domin biyan bukatun matafiya.

Biranen da fasinjoji suka fi bari a wannan lokaci sun hada da Guangzhou, da Beijing da Chengdu, yayin da biranen da fasinjoji suka fi komawa suka hada da Beijing, da Guangzhou da Shanghai. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *