Fashewar Bam Ta Girgiza Maiduguri, Ana Fargabar Mutane Sun Mutu
[ad_1]
An shiga fargaba a birnin Maiduguri bayan wasu fashewar bama-bamai da suka auku a kusa da kasuwar Monday Market Maiduguri da kuma wani wurin tsaro a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri.
Rahotanni sun ce bama-baman sun fashe kusan lokaci guda da misalin karfe 7:02 na yammacin ranar Litinin, lamarin da ya janyo fargaba a tsakanin mazauna yankin. Ana fargabar cewa wasu mutane sun mutu yayin da da dama suka jikkata sakamakon fashewar.
- Gwamnatin Tarayya Ta Yabawa Zulum Kan Faɗaɗa Ilimin Fasaha Da Sana’o’i A Borno
- Rarara Zai Angwance Da Aisha Humaira Yau A Maiduguri
Shugaban sashin ayyuka na Hukumar Kashe Gobara na jihar Borno, Mohammed Kafaran, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa sun tura jami’ansu zuwa wurin domin tantance halin da ake ciki.
Shaidu sun ce an garzaya da wasu daga cikin waɗanda suka jikkata zuwa asibitin kwararru na birnin Maiduguri domin samun kulawar likitoci, yayin da wasu suka ce sun ga gawarwaki a wurin abin fashewar.
Jami’an agaji da na tsaro na ci gaba da aikin ceto da tantance ɓarnar da fashewar ta janyo, yayin da ake sa ran ƙarin bayani kan lamarin nan gaba.
[ad_2]
Source link