An kama Ɗan sanda kan harbe soja a Bauchi

[ad_1]



An kama wani Jami’in ɗan sanda bisa kashe wani soja a garin Futuk da ke Ƙaramar hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi.

Muƙaddashin Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar soji, 33 Artillery Brigade, Atang Hallet Solomon, ya tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin.

Ya ce, jami’in da ake zargin ya harbe sojan har lahira an kuma tsare shi, inda ya ce a halin yanzu ana gudanar da binciken haɗin gwiwa tsakanin ’yan sanda da sojoji.

Hallet ya ce ana ci gaba da tattaunawa tsakanin hukumomin tsaron biyu domin tabbatar da gudanar da cikakken bincike da kuma hana afkuwar lamarin nan gaba.

Mafarauta da ’yan banga a garin Futuk sun ce lamarin ya biyo bayan cece-ku-ce tsakanin jami’an tsaro kan wata motar ɗaukar kaya da ake zargin na wani kamfanin haƙar ma’adinai na ƙasar China ne.

Sun ce, motar da ke ɗauke da ma’adanai daga wurin haƙar ma’adinai na Yalo, an kama ta ne da yammacin ranar Litinin jim kaɗan bayan sallar Magariba.

Shaidu sun ce sojojin na 33 Artillery Brigade da ke Bauchi sun umarci direban motar mai lamba Gombe 676 BLG da ya tsaya a wani shingen bincike da ke Futuk. Da direban ya ƙi amincewa, sai sojojin suka bi su suka tare motar a kusa da wata gada.

Wani da ya buƙaci a sakaya sunansa kuma shaida ne ya ce, a yayin musayar yawu tsakanin sojan da aka harbe da wani jami’in ’yan sandan kwantar da tarzoma (MOPOL) mai muƙamin Insfekta ya harbe wani soja har lahira a garin Futuk da ke Ƙaramar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *