Barayi sun yi awon gaba tan 12 na cakulat

[ad_1]



An sace tan 12 na cakulat ɗin KitKat, bayan da barayi suka yi awon gaba da motar da ke ɗauke da su a da nufin raba su a sassan kasashen nahiyar Turai a makon da ya gabata.

Kamfanin Nestlé da je kasar Switzerland ya bayyana cewa motar da aka sace tana ɗauke da sinki 413,793 na KitKat da ta ta tashi da su daga tsakiyar kasar Italiya domin rarraba su a sassan nahiyar Turai.

Kamfanin ya bayyana cewa motar ba ta kai ga inda aka nufa domin kammala rabon kayana a kasar Poland ba.

Har yanzu ba a gano inda motar ko kayan suke kaya ba, kuma kamfanin bai bayyana ainihin inda aka rasa su ba.

A wata sanarwa daban, KitKat ta ce ana iya gano sandunan da suka ɓace ta hanyar lambar batch code dinsu na musamman, inda duk wanda ya duba lambar zai samu umarnin yadda zai tuntubi kamfanin.

KitKat sun ce, “Ko da yake muna yaba wa zaɓin ɗanɗanon barayin, abin da ya faru na nuna yadda satar kaya ke ƙaruwa a kasuwanci a kowane mataki.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *