Wazirin Ningi Ya Yi Murabus Bisa Zargin Shigar Da Siyasa Cikin Harƙoƙin Masarautar

[ad_1]

Wazirin Masarautar Ningi, Babban Ɗan Majalisa (Senior Councillor), kuma Shugaban Masu Zaɓen Sarki na Majalisar Masarautar Ningi, Amb. Shuaibu Ahmed Adamu ya yi murabus daga muƙaminsa.

A cikin wata wasiƙa da tsohon Wazirin ya aike wa Sarkin Ningi, Alh. Haruna Yunusa M. Danyaya Mai kwanan wata 26 ga watan Janairun 2026 da wakilinmu ya ci karo da ita a ranar Alhamis, Ahmed ya ce, ya ɗauki matakin ne bisa zargin da ya yi na cewa siyasa ta shigo cikin harkokin gudanarwar Masarautar, musamman kan umarnin Gwamnatin Jihar Bauchi ta bayar wanda ya nemi a rage darajar matsayinsa na shugabancin masu zaɓen Sarkin masarautar.

  • Za A Gudanar Da Dandalin Tattaunawa Na Masana Na Jam’iyyar JKS Da KMT A Birnin Beijing
  • Majalisar Dattawa Ta Kai Ta’aziyya Ga Al’ummar Kurmin Wali, Ta Yi Alkawarin Kayan Agaji

Wasiƙar na cewa: “Cikin cikakken girmamawa da matukar alhini, ina miƙa wannan wasiƙa domin sanar da Mai Martaba cewa na yanke shawarar yin murabus daga muƙamina na Wazirin Ningi, Babban Ɗan Majalisa (Senior Councillor), da kuma Shugaban Masu Zaɓen Sarki na Majalisar Masarautar Ningi, wanda zai fara aiki daga 26 ga Janairu, 2026.”

“Kusan tsawon shekaru hudu (4) ke nan da Allah Subhanahu Wa Taála, Ya ƙaddara Majalisar Masarautar Ningi, tare da amincewar Gwanatin Jihar Bauchi, ta tabbatar min da wannan babban muƙamin mai alfarma, na Wazirin Ningi.

“Tun da aka naɗa ni Waziri na riƙe muƙamin bilhaƙƙi da gaskiya, tare da cikakken sadaukarwa, da girmamawa al’adunmu na gargajiya. A matsayi na na Shugaban Masu Zaɓen Sarki, wanda wani nauyi ne da na riƙe cikin girmamawa da darajawa, na samu nasarar sauƙe nauyin jagorantar tsarin zaɓen Sarki cikin tsoron Allah, da kuma bin ƙa’idodin da doka ta tsayar.”

Ya ci gaba da cewa, “Shawara ta ta yin murabus daga matsayin Wazirin Ningi ba abu ne mai sauƙi ba ko kaɗan. Na yanke shawarar ne bayan dogon nazari da tunani kan abubuwan da suka faru kwanan nan yadda siyasa ta shigo cikin harkokin gudanarwar Masarautarmu, musamman kan umarnin da ya fito daga Gwamnatin Jihar Bauchi wanda ya nemi a rage darajar matsayina na Shugabancin Masu Zaɓen Sarki.

“Wannan umarnin ba sakamakon yarjejeniya ko buƙatar gudanarwar Majalisar Masarauta ba ne, illa dai sakamakon zagon-ƙasa na siyasa daga waje, ta hannun wasu da ke kusa da fadar Gwamnatin Jihar Bauchi.

“Abin takaici shi ne yadda Mai Girma Gwamna Sanata Bala Mohammed, ya gaggauta amincewa da burin wannan masu zagon-ƙasa, sannan ya umarci Mai Martaba da ku bayar da shawarar waɗannan canje-canjen,” in ji shi.

“Kan haka ne naga ba zan iya ci gaba da aiki na ba, ba tare da na saba wa ƙa’idodin da na rantse zan kare ba. Amincewa da wannan matsayi da aka rage wa daraja zai zama tamkar na yarda da sanya siyasa a cikin al’adun Masarauta,” ya nanata.

“Ina fata da gaske cewa tafiyata za ta zama sanadin yin tunani mai zurfi a cikin Majalisar Masarautar Ningi, da ma dukkan Masarautun dake faɗin Arewacin Nijeriya, tare da aika sako ga ‘yan siyasa masu son raunana tushen tarihinmu.”

“Na ji daɗin aiki ƙarƙashin Marigayi Sarki, Mai Martaba Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya (Allah ya jikansa da rahama), sannan tun bayan naɗin ka, na ci gaba da aiki tuƙuru da sadaukar da kai ƙarƙashin ka, Mai Martaba Sarki Haruna. Har abada zan kasance mai godiya da irin yarda da kwarin gwiwar da Majalisar Masarauta, da kuma daukacin al’ummar Ningi suka ba ni.”

Ya nuna matukar godiya ga Allah (SWT) kan ɗimbin ni’imomin da ya yi masa, “Alhamdu Lillah, a tsawon lokacin da na yi ina Wazirin Ningi, na yi iyakacin ƙoƙari na wurin riƙe gaskiya da kauce wa zalunci.”

Ya nanata cewa zai ci gaba da kasancewa mai biyayya ga Masarauta da kishin al’ummar Ningi baki ɗaya.

“Ina rokon Allah Ya bamu zaman lafiya da ci gaban Masarautar Ningi da al’ummarta. Allah kuma Ya bawa Mai Martaba Sarki da Al’umar Masarautar Ningi hakuri kan wannan al’amari. Amin!”.

Amb. Shuaibu Ahmed Adamu ya kuma aike da kwafin wasiƙar ga Gwamnan Jihar Bauchi da Shugaban Hukumar Hidimar Ƙananan Hukumomi, Jihar Bauchi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *