Dole Ne Duniya Ta Hana Sake Farfado Da Tsarin Amfani Da Karfin Soja Na Japan

[ad_1]

A farkon watan Nuwambar bara, Firaministar Japan Sanae Takaichi ta yi ikirari a bainar jama’a lokacin wani zaman majalisar dokokin kasar cewa, abin da ake kira da “makomar Taiwan” na iya zama wani “yanayi mai barazana ga dorewa” wanda zai ba Japan damar amfani da ‘yancin kare kai na gaba daya.

Wannan shi ne karo na farko tun bayan kayar da Japan a shekarar 1945 da wani shugaban kasar mai ci ya gabatar da ra’ayi a hukumance na cewa “makomar Taiwan wani lamari ne da zai iya shafar makomar Japan” yayin da yake danganta hakan da amfani da ‘yancin kare kai na gaba daya. Wannan kuma shi ne karo na farko da Japan ta bayyana burinta na tsoma baki bisa amfani da karfin soji a kan batun Taiwan, kuma karo na farko da Japan ta yi barazanar tilasta wa kasar Sin.

A tarihi, lokacin da take neman fadada kasarta, masu ra’ayin amfani da karfin soja na Japan sun rika nuna Japan a matsayin kasar da aka zalunta wacce ba ta da wani zabi, suna karkatar da gaskiya don neman goyon baya a cikin gida. Yanayi na bayar da dama sai suka kaddamar da yake-yake ba tare da la’akari da abokan hamayya ba, ko mummunan sakamako, ko sanarwa, ko kuma hanyoyin da za a yi amfani da su. Tunanin amfani da karfin soja yana ci gaba da ba da damar yin kalamai da ayyuka na ganganci ga shugabannin Japan na yanzu.

Tsarin Japan na amfani da karfin soji ya haifar da yake-yake na zalunci na kasar kuma ya kasance tushen akidar masu tsattsauran ra’ayi na kasar.

Katobara da wasu ayyuka na Takaichi da sauransu ba abubuwa ne da suka zamo daban da na baya ba ta kowace fuska. A cikin ‘yan shekarun nan, Japan ta kara yawan kudin da take kashewa na tsaro har na tsawon shekaru 13 a jere, ta sassauta takunkumi kan aiwatar da manufar tsaron kai ta gaba daya, sannan sau da yawa ta sassauta dokar hana fitar da makamai, kana tana yunkurin aiki da abin da aka kira da “karfin dakile kawo hari,” har ma ta nemi yin gyara ga ka’idoji uku da ba su shafi sha’anin nukiliya ba.

Kudurin amfani da karfin soji na Japan hadari ne na gaske kuma mai bukatar matakin gaggawa. Idan Japan ta ci gaba da bin wannan muguwar hanya, duk kasashe da al’ummomin da suka himmatu ga tabbatar da adalci suna da ‘yancin sake duba miyagun laifukan Japan na tarihi da kuma sauke alhakin hana sake farfado da tsarin amfani da karfin soja. Wannan babban batu ne ga al’ummomin duniya wajen kare tsarin kasa da kasa da aka samar bayan yakin duiya na biyu da kuma gwaji na hakika don gano ko ita kanta Japan za ta iya ci gaba da raya zaman lafiya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *