Allah Ya Bai Wa Annabi (SAW) Mu’ujizozi Fiye Da 2,000 A Alƙur’ani

[ad_1]


… ci gaba daga makon da ya gabata.

Tanan za a fahimci cewa, duk masu ikirarin guluwwi da tahdidi karya suke, duk wannan aya ta “caffa da Annabi” da Ubangiji ya ce, da shi aka yi, ta karyata su.

4 – Allah ya hada girmansa da girman Annabinsa (Walillahil izzatu wali rasulihi…), ya kara hada yardarsa da yardar Annabinsa (Wallahu warasuluhu a hakku an yurduhu), Allah da Annabinsa shi yafe cancanta a yarda da shi. Ubangiji in yana magana da Annabinsa, lamiri daya yake amfani da shi ba na mutum biyu ba. Wani Hadisi ya zo, yana bayar da labarin wani abu da ya faru tsakanin wanin masanin zance da Annabi SAW, kila an ce ya Annabin Allah, ga wani masanin zance yana so zai yi maka zance, sai aka amince masa hakan, daga cikin zancensa, ya bayyana cewa, “duk wanda ya yi wa Allah da Annabinsa biyayya, ya tsira; wanda duk ya bijerewa Allah da Annabinsa, ya hallaka, (Man Adahuma fakad rashada, wa man Asahuma fakad gawa)”, sai Annabi SAW ya kore shi. Da yawan

Malamai masu sharhin wannan Hadisi, suna cewa, wannan hukuncin Annabi ne da ya zartar amma su ba su ga kuskuren da ya yi ba. Bangaren Sufaye suka amsa cewa, sun gano inda ya yi kuskure, Ubangiji in zai hada kansa da Annabinsa, Lamirin abu daya yake amfani da shi amma wannan masanin zance, da Lamirin abu biyu ya yi amfani da shi a gaban Annabi SAW da fadinsa (Adahuma da Asahuma a maimakon Adahu da Asahu). Amma Annabi SAW da ya iya karatun, cewa ya yi, “Allah wa rasuluhu harrama bai’al Kamri – Allah da ma’aikinsa ya hana kasuwancin giya”, don haka, duk wanda ya ce, zai rabe tsakanin Allah da Annabinsa, to ya kuka da kansa.

Al’ummar Annabi SAW, Malama ce wayayya, ba za ta taba daukar Annabi SAW ya zama kishiyar Allah ba. Mutum ne mai girma da Allah ya girmama shi. Don kana tarayya da wani babban mutum aka da yaushe, ba zai sa ka zama shi ba. Annabi SAW wani mai girma ne da Ubangiji ya girmama shi har karatu ya kasa fahimtar kusancin shi da Ubangiji (Dana fatadalla, fakana kaba kausaini au adna).

5 – Allah ya saka amsa masa, amsa wa Annabinsa ne SAW (Ya Ayyuhallazina amanu istajibu lillahi walirrasuli iza da’akum – ya ku wadanda kuka yi imani, ku amsa kiran Ubangiji da na Annabinsa idan sun kira ku…

6 – Allah Ubangiji ya hori Annabi SAW ya yi fito-na-fito da kowace sura ta Alkur’ani, mafi karamar sura ta Alkur’ani, itace me aya Uku (Suratul Kausar), don haka, kowace sura a Alkur’ani ta zama “Mu’ujiza”,  da wannan lissafi za mu fahimci cewa, duk aya Uku ta Alkur’ani Mu’ujiza ce!

Muhyiddeen Arabi, ya ce, duk Aya Daya fannin wani ilimi ce, Shehu Ibrahim Inyass ya ce gaskiya ne amma akwai aya Daya na samu fannin ilimi tara acikinta, itace (Falizalika fad’u, wastakim kama umirta, wala tattabi’i ahwa’ahum, wakul amantu bima anzalallahu minal kitab, wa umirtu li a’adila bainakum, Allahu rabbuna wa rabbukum, lana a’amaluna walakum a’amalukum, la hujjata bainana wa bainakum, Allahu yajma’u bainana, wa ilaihil masir – yi kira akan wannan alkairan da aka baka, tsaya kamar yadda aka umurceka, kar ka bi son zuciyarsu, ka ce ka yi ka yi imani da abinda Ubangijinka ya saukar maka daga Alkur’ani, an umarce ni in yi adalci a tsakanin ku, Allah shi ne Ubangijinmu kuma shi ne Ubangijinku, babu wanda za a yi masa hisabi da aikin wani na sharri amma alkairin wasu na shafar wasu, babu wata hujja tsakaninmu da ku, Allah zai hada mu daku a ranar Alkiyama, duk wurin Ubangiji dai za mu tafi.

Mu tafi a cewa, duk aya Uku, mu’ujiza ce, akwai ayoyi fiye da 6,000 a Alkur’ani, in muka raba 6,000+ gida uku, za mu samu mu’ujiza 2,000+ acikin Alkur’ani.

Annabi Musa AS, Ubangiji ya ambace shi da cewa, ya ba shi mu’ujiza 9 amma Annabi SAW, a Alkur’ani mun samu 2,000+. Don haka, ba sai an yi tawili ba, a fili yake, Annabi SAW ya fi duk sauran Annabawan Allah. Sannan kuma, duk mu’ujizozin sauran Annabawa, zamani na tsawo suna kara shudewa, amma na Annabi SAW zamani na tsawo suna kara bayyana.

Cewa, mu’ujizozin Annabi SAW sun fi na sauran Annabawa, hakan ya nuna cewa, ya fi duk sauran Annabawa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *