Yau Shugabannin Tsaron Afrika 54 za su yi taro a Abuja

[ad_1]



A yau Litinin Najeriya take karbar baukuncin Shugabannin tsaron kasashen Afirka 54 a binrin Abuja, inda za su tattauna hanyoyin magance matsalolin tsaro da suka addabi nahiyar.

Za a gudanar da taron ne a karkashin jagorancin Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, kuma Shugaban Kasa Bola Tinubu zai bude shi.

Janar Musa ya ce taron, wanda shi ne na farko irinsa, zai bai wa shugabannin soji na Afirka damar tattauna matsalolin tsaro a fili tare da tsara hanyoyin magance su ba tare da dogaro da kasashen waje ba.

“Mun dade muna neman mafita daga waje, abin da ya kara tsawaita matsalolinmu. Magana ta gaskiya ita ce, mafita tana cikinmu, mu ne za mu samar da ita,” in ji Janar Musa.

Ya ce taron zai kuma duba batun rundunar sojin hadin gwiwar kasashen Afirka wadda har yanzu ba ta samu cikakken tsari ba, saboda matsalolin kudi da tsasre-tsare.

Fiye da kashi 90 cikin 100 na kasashen da aka gayyata sun tabbatar cewa za su halarci taron , kana manyan jami’an Majalisar Dinkin Duniya da tsoffin hafsoshin tsaro da kwararru a harkokin tsaro za su halarta.

Musa ya ce burin taron shi ne ganin nahiyar Afirka ta samu tsaro da ci gaba da kuma wanda ’ya’yanta ke jagorantar makomarta.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *