Wang Yi Da Takwaransa Na Kamaru Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Huldar Diflomasiyyar Kasashen 2

[ad_1]

Yau Alhamis, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaransa na kasar Kamaru Mbella Mbella Lejeune sun mika wa juna sakon taya murnar cika shekaru 55 da kulla huldar diflomsiyya a tsakanin Sin da Kamaru.

Wang Yi ya ce, cikin shekaru 55 da suka gabata, Sin da Kamaru sun nuna goyon baya ga juna, da kuma neman ci gaba tare. Cikin ’yan shekarun nan, bisa jagorancin shugaba Xi Jinping da shugaba Paul Biya, an ci gaba da kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu kamar yadda ake fata, da zurfafa fahimtar juna ta fannin siyasa a tsakanin kasashen biyu, da cimma sakamako da dama kan fannoni daban daban, tare da yin hadin gwiwa wajen gudanar da harkokin kasashen duniya yadda ya kamata.

Haka kuma, Wang Yi ya ce, yana fatan yin hadin gwiwa da mista Lejeune wajen aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da sakamakon da aka cimma a taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, wanda ya gudana a birnin Beijing, domin inganta dangantakar abokantaka a tsakanin Sin da Kamaru bisa manyan tsare-tsare.

A nasa bangare kuma, Mbella Mbella Lejeune ya ce, Kamaru za ta dukufa wajen zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu, da karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu domin tallafa wa al’ummomin kasashen Sin da Kamaru. (Mai Fassara: Maryam Yang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *