2027: Atiku Da Makinde Sun Yi Ganawar Sirri Da IBB

[ad_1]

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, da Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, sun kai ziyara daban-daban ga tsohon shugaban soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya), a gidansa na Hilltop a Minna, Jihar Neja, a yayin da ake samun karuwar tattaunawar siyasa kafin zabukan 2027.

Atiku da Makinde sun isa gidan Babangida a lokuta daban-daban. Tsohon mataimakin shugaban kasa ya sauka a Filin Jirgin Sama na Bola Ahmed Tinubu, Minna, daidai karfe 12:46 na rana, a kan jirgi mai zaman kansa mai lamba 5N-KAS.

  • CGTN: Mafarkin Amurka Ya Lalace Zuwa Rudi Na Cin Zali
  • Mu’amala Tsakanin Shugabannin Sin Da Amurka Tana Taka Muhimmiyar Rawa A Dangantakar Kasashen

Ya samu rakiya daga shugabanni ciki har da Kashim Imam da Sanata Ben Obi.

Gwamna Makinde ya isa gidan Babangida a kusan karfe 2:00 na rana, tare da tsohon gwamnan Jihar Osun, Olagunsoye Oyinlola.

Atiku ya yi tattaunawa ta musamman da Babangida fiye da awanni biyu, sannan ya tashi daga Minna a kusan karfe 3:20 na rana. Makinde, a gefe guda, ya tsaya a gidan har kusan karfe 4:00 na rana bayan karin lokaci da ya yi tare da tsohon shugaban mulkin soja.

Majiyoyi sun shaida wa Daily Trust cewa ziyarar Atiku na neman goyon bayan Babangida ne domin ADC, yayin da Makinde kuma ya tattauna da tsohon shugaban soja kan shirin da ake cewa zai shiga jam’iyyar.

Bayan taron, Atiku ya ce ziyarar wani bangare ce ta kokarin karfafa goyon bayan ‘yan Nijeriya ga ADC da kuma rajistar sababbin mambobi, tare da karfafa tsarin jam’iyyar a kasar baki daya.

Ya tabbatar da mambobinsa a ADC kuma ya bayyana cewa kundin tsarin jam’iyyar bai amince da raba yankuna ba (zoning).

“Babu zoning a kundin tsarin jam’iyyar ADC. A gaskiya, PDP ce kawai ke da zoning a cikin kundinta,” in ji shi.

“Ba wannan ne karo na farko da na ziyarci Minna ba. Na kasance ina zuwa a koda yaushe don girmamawa. Batun takara a 2027 har yanzu bai taso ba,” Atiku ya kara da cewa.

Ya ce jam’iyyar ADC na mai da hankali ne wajen gina ingantattun tsare-tsare daga matakin unguwa har zuwa na kasa, tare da karfafa rajista da jawo sababbin mambobi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *