Yadda mata ke sauya akalar tsaro a Kano

[ad_1]



A tsarin al’ummar Hausawa, ana kallon mace a matsayin mai zaman gida da kuma kula da iyali da tarbiyya. Don haka shigarsu ayyukan da ke buƙatar fitar dare, tafiya mai nisa, sanya sutura iri ɗaya da maza ko hulɗa kai tsaye da su kan zamo abun magana.

Wannan ya taka rawa wajen taƙaita damarsu ta shiga irin waɗannan ayyuka. Idan ma suka shiga, galibi suna taƙaita ne ga aikin zaman ofis ne ko na bayan fage.

Aikin ɗamara ko na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma an fi danganta su da maza saboda tasirin al’ada da addini. Wannan ne ya sa yawanci, idan mace ta shiga aikin tsaro, ake mata wani kallo na daban.

Rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya (UN Women da UNDP) ya nuna cewa mata ba su fi kashi 20% ba na ma’aikatan tsaro a faɗ Afirka ta Yamma. A Nijeriya kuma, alƙaluman Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) sun bayyana cewa al’ada, addini da tsoron cin zarafi sun sa mata na gudun shiga aikin tsaro, musamman a Arewa. Wasu rahotanni sun kuma nuna cewa ko da matan sun shiga, yawanci ba a ba su damar shiga manyan ayyukan tsaro ko na fili.

Sai dai da alama gwamnatin Kano ta hango giɓin da hakan ya haifar ga tsaron jihar, da kuma irin gudummawar da mata za su iya bayarwa wajen shawo kan matsalolin satar mutane, ƙwacen waya da satar ababen hawa.

Gwamnatin ta ɗauki mata 130 daga cikin jami’ai 2,000 da ta bai wa horon tabbatar da tsaron rayuka da kuma samar da bayanan sirri a matakin unguwanni, wato NWC, a cikin matakanta na ƙarfafa tsaro daga tushe, ta hanyar amfani da mutanen da suka san unguwanni, hanyoyi da al’adun jama’a sosai.

Binciken Aminiya ya gano cewa shirin horas da jami’an NWC ya fara ne tun a watan Mayun shekarar da ta gabata, inda aka tantance mutane da dama, aka gudanar da gwajegwajen lafiyar jiki da tunani, tare da horaswa mai tsanani ƙarƙashin kulawar jami’an tsaro na gwamnati, ciki har da sojoji da ’yan sanda.

Wani jigo a NWC ya shaida wa Aminiya cewa an gudanar da komai ne ba tare da kwarzantawa ba saboda muhimmancin sirri a aikin samar da tsaro.

A watan Disambar 2025, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da jami’an a hukumance, a wani biki da ya jagoranta a Filin Wasa na Sani Abacha da ke unguwar Ƙofar Mata.

Kan haka ne Aminiya ta tattauna da wasu mata guda uku daga cikin jami’an — Amina Sani Usman daga Ƙaramar Hukumar Kumbotso, Aisha Abdulmutallab daga Nassarawa, da Hassana daga Tarauni. Sun bayyana irin ƙalubalen da suka fuskanta da kuma nasarorin da suka samu, yayin da aka shiga mako na biyu da fara aikin.

Yadda na jagoranci kama mai garkuwa da mutane — Hassana

Ga Hassana ƙalubalen da ta fuskanta ya daga gida ne, inda dangin mahaifinta suka nuna rashin amincewa da shiga aikinta, saboad suna ganin aikin tsaro bai dace da mace ta ba, musamman wanda ke buƙatar fita da yamma ko mu’amala da maza, da yin shigar da ta saɓa wa al’ada. Amma mahaifiyarta, a cewarta, ta tsaya tsayin daka wajen ƙarfafa mata gwiwa, tana mai tunatar da ita cewa aiki na halal ne kuma na hidimar al’umma ne.

Hassana ta ce bata taɓa yin nadama ba, domin fara aikinta ke da wuya ne ta samu babbar nasarar taimaka wa jami’an ’yan sanda wajen kama wata mata mai garkuwa da mutane da ta tsallako daga Katsina zuwa Jihar Kano.

Lamarin ya faru ne a lokacin da Hassan take kan hanyarta ta yin tafiya, inda wata mata da ta zauna a kusa da ita ta hau ba ta labaran satar mutanen da take yi da suka ɗaga mata hankali.

“Duk da tsoron da ya kama ni, na yi hikima wajen ɗaukar hoton matar bayan na kirawo shugabana a waya ya ƙarfafa min gwiwa. Bayan ya sanar da ni cewa akwai shingen binciken ’yan sanda a gaba da mu, da mun isa wajen na haɗa ta da jami’an tsaro. Haka kuwa aka yi,” in ji ta.

Ta ƙara da cewa bayan kama matar, ta shiga firgici har zuwa lokacin da ta koma gida, amma daga baya ta ji daɗin ganin an daƙile wani mummunan laifi.

“Wannan bajintar ta sa na samu lambar yabo sosai daga jagororinmu da sauran abokan aiki,” in ji ta.

Ta ce wannan na nuna muhimmancin shigar mata aikin tsaro, domin suna da damar samun bayanai a wuraren da maza ba sa iya shiga ba cikin sauƙi kamar mu’amalar mata.

‘Ji na nake kamar namiji’

Amina Sani Usman, jami’ar NWC daga Ƙaramar Hukumar Kumbotso ta ce burinta na shiga aikin ɗamara ya samo asali ne tun tana ƙarama. Ta ce duk da al’umma ba su fiye goyon bayan mata su yi aikin ɗamara ba, kuma ko sun shiga, sukan ɓoye kansu saboda tsoron kalaman jama’a, hakan bai hana ta cimma burinta ba.

“Da na ji ana neman mata, sai na nema, kuma na yi dace na samu,” in ji Amina, tana mai cewa tun a wajen tantancewa wasu suka karaya saboda wahala.

Ta ce ɗaya daga cikin abubuwan da ya fara sanya ta fahimtar cewa ta shigo fagen maza, shi ne horon da suka samu ƙarƙashin sojoji, wanda ta ce ya kasance mai matuƙar wahala, musamman ga ’ya mace, inda aka gwada juriyarsu ta kowace fuska — ta jiki, ta tunani da ta haƙuri.

“Barci a ƙayyade yake, sannan tun daga bakin ƙofa za ka san ka zo wurin da babu wasa a cikinsa, domin a kai za ka ɗora kayanka ka shiga har cikin sansanin da su, duk nauyinsu,” in ji ta, tana mai cewa akwai lokutan da suke samun horo cikin ruwan sama ko tsananin zafi ko sanyi, sallah da cin abinci kaɗai ke tayar da su.

Ta ce, “Duk da haka, cikin mata kusan 100 da aka fara horaswa, babu wacce ta fice saboda wahala sai maza wajen guda uku. Don akwai wanda ya fashe da kuka ma ya ce a sallame shi ya haƙura. Sai da sojojin suka dinga lallashin sa ya haƙura.”

Wannan, a cewar Amina, ya ƙara mata ƙarfin gwiwar jajircewa.

Amma duk da haka, ta ce aikin ya wuce yadda ta yi tsammani, kuma an samar musu da kayan aiki tare da mutunta addini da al’ada, inda aka ba su damar sanya hijabi ko mayafi yayin aiki.

“Duk da haka, idan na sa kakin nan, ji na nake kamar namiji,” in ji ta cike da farin ciki.

Tun ina yarinya nake son aikin tsaro — A’isha

A cewar Aisha Abdulmutallab daga Ƙaramar Hukumar Nassarawa, samun aikin NWC ya zo mata ne bayan ɗaukar dogon lokaci tana neman aiki.

Ta bayyana cewa ta sha nema ba tare da ta samu nasara ba, lamarin da ya sa ta ji ƙwarin gwiwa da godiya lokacin da aka ɗauke ta cikin wannan tsari.

Ta ce ta bi matakai masu tsauri kafin ta samu cika burinta, ciki har da tantancewar lafiyar jiki, horon ɗabi’a da kuma gwajin juriyar aiki.

A halin yanzu dai, Aisha na cikin rukunin Ƙuarter Guard — waɗanda aikinsu ya haɗa da yi wa sara wa manyan baƙi da bindiga a lokutan bukukuwa da tarurruka na gwamnati. Ita ce Kurfo, mai riƙe sanda, yayin da sauran abokan aikinta tara ke ɗauke da bindigogi.

“Ina alfahari da aikina,” in ji ta

Sai dai horon yin wannan aikin da mutane ke ganin ba mai wahala ba ne bai zo mata da sauƙi ba. Ta ce an bar su a rana tsawon makonni biyu domin su koyi jure zafi da sanyi, tare da horon doguwar tafiya, doguwar tsayuwa ta sa’o’i, da bin umarni ba tare da ɓata lokaci ba.

Ta ce, “Na sha wahala kafin na saba,” tana mai jaddada rawar da mahaifiyarta ta taka wajen ba ta shawara da haƙuri, tana faɗa mata cewa duk wata wahala tana da ƙarshe.

Labarin Amina, Aisha da Hassana ya nuna cewa mata na iya taka rawar gani a tsaro idan aka ba su dama. Wannan sabon tsarin na Neighbourhood Watch Corps, ya zama ginshiƙin sauyi a fannin, domin ya sauya kallon da wasu ke yi wa mata — daga masu buƙatar kariyar maza kaɗai zuwa masu bayar da kariya da tsaron al’umma.

Masana harkar tsaro da walwalar al’umma na ganin cewa shigar mata cikin tsaron al’umma zai ƙara wa tsarin inganci, musamman wajen tattara bayanai da gina amincewa tsakanin jami’an tsaro da jama’a. A Kano, inda al’ada da addini ke taka muhimmiyar rawa a rayuwar yau da kullum, wannan mataki na iya zama farkon wani sabon babi a tarihin jihar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *