Masu Sayar Da Abinci Da Tsada, A Ji Tsoron Allah
[ad_1]
Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu.
Jama’a barkanmu da kasancewa tare da wannan fili mai albarka, filin da yake zakulo batutuwan da suke ci mana tuwo a kwarya.
A wannan gabar zan yi wani dan tsokaci ko nace tuni ko kuma jan hankali, musamman game da masu siyar da kayan abinci na cikin lunguna ko na shaguna.
Idan muka yi duba da ‘yan watannin nan cikin lokutan nan, za mu ga cewa kayan abinci suna yin sauki kuma suna karyewa, sai dai wani hanzari ba gudu ba masu dafa abinci su siyar suna siyar wa da tsada ba tare da sun kara mudu ba, ma’ana; ba sa yin aunin daidai yadda ya kamata.
Ya ilahil’alamina yaushe rayuwa za ta yi daidai, abu na farko dai tauye mudu haramun ne, domin Manzon Allah (SAW) a hadisansa ingantattu ya yi magana sosai akan irin azabar da wadannan mutanen za su sha a ranar gobe alkiyama.
Ya kamata masu auna mudu su rika aunawa daidai misali, kuma ha’inci ne idan ka tauye mudu ko ka rage yadda ake auna mudu, ranar gobe alkiyama za ka biya, kuma za ka fuskanci hukuncin ubangiji.
Haka mutanen da suke siyo danyan abinci a saukake, sai su siyar da shi da tsada su zuga masa kudi ko da kuwa ya sakko dan kawai su ci riba, wannan ba riba bace ribau ce, kuma shi ma haramun ne. Ya kamata mu ji tsoron Allah, tsadar abinci ma musifa ne.
Akwai masu shaguna na lungu da sako wasu wuraren ba sa saukaka wannan al’amarin ko kadan, ya kamata dai mu duba. Idan ka tausaya sai Allah kai ma ya tausaya maka, ba sai kayi tsada za ka yi kudi ba, ba a yin arziki a haka, idan ka tausaya sai Allah ya kalli zuciyarka.
Ina kara jan hankalin mutane musamman masu aikata hakan, da masu sha’awar yin hakan, dan Allah a tausaya a wannan bangare na siyan abinci, idan ka samu a sauki kai ma sai ka siyarwa al’umma a saukake su samu sauki, idan farashi ne ya dagu kai ma sai ka daga.
Amma sai a ga kayan abinci ya sakko, masu dafa abincin siyarwa awon bai ragu ba kuma bai karu ba, sun kara masa kudi, ai ya kamata ace tunda abinci ya sakko suma a wajensu abun yayi sauki. Da yawa wuraren da ake siyar da abinci haka suke, sun kara kudin kuma sun ki kara awon da suke na abincin, wannan zalumci ne, kuma babu kyau, rashin tausayi ne.
Idan ka tausaya Allah zai tausaya maka, ba kullum ka rika zagin shuwagabanni ba, abinci ya sakko kai ba za ka sakko da naka ba. Jama’a duk sai mun ji tsoron Allah, mu kyautata sai mu ga daidai, Allah ya sa mu dace.
[ad_2]
Source link