Zan Tabbatar Duk Ƴan Dakon Hatsi A Nassarawa Sun Mallaki Katin Zaɓe — Alhaji Danji
[ad_1]
Shugaban Ƙungiyar ƴan Dakon Hatsi ta Jihar Nasarawa, Alhaji Danji Aliyu, ya ce zai gudanar da rangadi a dukkan ƙananan hukumomin jihar domin tabbatar da cewa duk mambobin ƙungiyar sun mallaki katin zaɓe.
Alhaji Danji ya bayyana hakan ne a ofishinsa da ke Lafia, bayan kammala taron addu’ar shiga sabuwar shekarar 2026. Ya jaddada cewa katin zaɓe hakki ne na kowane ɗan ƙasa, wanda ke ba shi damar zaɓar shugabannin da yake ganin za su yi masa adalci.
- Kotu Ta Dakatar Da Yunkurin Aminu Ado Bayero Na Gyaran Fadar Nassarawa
- Jam’iyyar NNPP Ta Yi Watsi Da Dakatarwar Da Aka Yi Wa Dungurawa A Kano
Ya ce ƙungiyar ƴan dakon hatsi na da mambobi masu yawa a faɗin jihar, kuma an ƙuduri aniyar tabbatar da cewa kowane mamba, tare da iyalansa, sun mallaki katin zaɓe domin shirye-shiryen zaɓe na gaba. Ya kuma gode wa mambobi da tsofaffin shugabannin ƙungiyar bisa amincewar da suka sake ba shi na jagorantar ƙungiyar na tsawon ƙarin shekaru uku.
A nasa jawabin, Shugaban ƙungiyar ƴan dakon hatsi ta ƙasa, Alhaji Hamza Abdullahi, ya shawarci mambobin da su rungumi yin tattali don gaba. Ya ce duk abin da mutum ya samu daga aikin dakon hatsi, ya ware wani kaso domin ajiya, yana mai jaddada cewa hakan zai taimaka musu su fara kasuwanci a nan gaba, musamman ganin cewa aikin na buƙatar ƙarfi wanda kan ragu da lokaci.
An gudanar da taron addu’ar ne a ranar 1 ga Janairu, 2026, a zauren ofishin ƙungiyar da ke kasuwar kayan hatsi ta Kwandare a Lafia, inda malamai da dama suka yi addu’o’i ga ƙungiyar, da shugabanninta, da Jihar Nasarawa da ƙasa baki ɗaya.
[ad_2]
Source link