’Yan bindiga sun sace shanu sama da 500 a kasuwar dabbobi a Zamfara

[ad_1]



’Yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun sace sama da shanu 500 a Kasuwar Daji da ke ƙaramar hukumar Kauran Namoda a jihar Zamfara.

Shugaban ƙungiyar Makiyaya ta Najeriya (CBAN), Comrade Aminu Garba, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce wannan ba shi ne karo na farko ba.

“Ba wanda ya yi tsammanin wannan zai faru. Mun fuskanci irin wannan mummunan lamari shekaru huɗu da suka gabata,” in ji shi.

Garba ya ce ana zargin ’yan bindigar sun shiga kasuwa da kauyukan da ke kewaye tun da rana, suna sa ido kan harkokin saye da sayarwa kafin su kai farmaki da dare.

Ya ƙara da cewa dabbobin da aka sace sun haɗa da shanu da aka sayo daga kasuwanni daban-daban, har da waɗanda aka kawo daga Jamhuriyar Nijar, domin Kasuwar Daji ita ce babbar kasuwar dabbobi a yankin.

“A kullum muna fara sayen dabbobi tun ranar Laraba kafin ranar kasuwar Daji, sannan mu tura su Legas,” in ji shi.

A cewarsa, ’yan bindigar da adadinsu ya kai akalla 50, dauke da makamai masu ƙarfi, sun kai farmaki da dare suka tafi da shanun zuwa yammacin kauyen, inda ake samun daji.

A wata hira dabam, ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, Alhaji Sani Yaba Ajiyan Fawa, ya ce ’yan bindigar sun fi 100.

Ya ce shanun da aka sace na hannun makiyaya da ake kira Yantugu.

Ajiyan Fawa ya ce an samu dawo da shanu kusan 60, waɗanda suka fantsama lokacin harin.

“Kamar yadda kuka sani, ba sauƙi ne a riƙe manyan dabbobi a cikin rikici ba. Waɗanda aka dawo da su su ne waɗanda suka watse lokacin harin,” in ji shi.

Game da jami’an tsaro da ke da sansani a ƙasa da mita 200 daga kasuwar, Ajiyan Fawa ya ce ba su yi wani yunƙuri ba har sai ’yan bindigar suka tafi da shanun.

Garba ya danganta rashin saurin ɗaukar matakin jami’an tsaro da rashin wayewar masu kula da dabbobin wajen neman taimako.

“Mutanen da ke kula da shanun ba su da ƙwarewar da za su nemi taimakon jami’an tsaro,” in ji shi.

Ya ƙiyasta asarar kuɗi da aka yi sakamakon harin ya haura Naira 500,000,000 yana mai cewa shanun da aka sace na hannun mutane da dama, wasu ma mallakar mutane da yawa ne.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *