Amurka ta kama shugaban ƙasar Venezuela a ƙasarsa

[ad_1]



Shugaban Donald Trump na Amurka, ya sanar da kama Shugaban Ƙasar Venezuela, Nicolas Maduro, tare da matarsa, kuma ta fitar da su daga ƙasar a safiyar Asabar.

Trump ya ce dakarun sojin Amurka sun tasa ƙeyar Mista Maduro rate da matarsa ne “bayan babban farmakin” da aka kai a Caracas, babba birnin ƙasar Venezuela.

Jim kaɗan bayan fitar sanarwar, Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Christopher Landau, ya bayyana cewa Shugaba Maduro, “zai fuskanci hukunci kan laifuffukansa.”

Gwamnatin Amurka tana zargin Mista Maduro da hannu a ayyukan Safar miyagun ƙwayoyi, zargin da tuni Mista Maduro ya ƙaryata.

Kama shugaban ƙasar da Trump ya sanar ta jawo tambayoyi kan matsayin Venezuela na ƙasa mai cikakken ’yanci.

Tun da farko, gwamnatin Venezuela ta zargi Amurka da kai hare-hare kan wuraren farar hula da cibiyoyin soja a jihohi da dama, tana mai ƙin amincewa da abin da ta kira “harin soja” daga Washington.

Gwamnatin Shugaba Nicolas Maduro ta ayyana dokar ta-ɓaci a fadin ƙasar bayan jerin hare-haren da aka kai.

Hare-haren sun faru ne bayan watanni na taƙaddama tsakanin Amurka da Venezuela, inda Amurka ta zargi Shugaban Venezuela, Nicolas Maduro, da hannu a safarar miyagun ƙwayoyi. Sai dai Mista Maduro ya musanta wannan zargi.

A ranar Alhamis, ya nuna cewa ƙofarsa a buɗe dom tattaunawa da Amurka domin cimma matsaya kan yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi.

Tun daga watan Satumba zuwa yanzu, Amurka ta kai sama da hare-haren jiragen yaki 20 a cikin teku kusa da Venezuela, tare da ƙaƙaba wa ƙasar takunkumi da ƙara matsin lamba na soja.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *