Za A Biya Super Eagles Kyautar Miliyan 14.5 Kan Kowace Ƙwallon Da Suka Ci A Wasa Da Mozambique
Tawagar Super Eagles ta Nijeriya za ta samu kyautar kusan dala 10,000 (kimanin naira miliyan 14.5) kan kowace ƙwallo da ta zura a wasan da za ta fafata da ƙasar Mozambique a yau Litinin, a filin wasa na Fes da ke Morocco. Wasa na cikin zagaye na 16 na gasar cin kofin nahiyar Afrika ta AFCON 2025.
Rahotanni sun nuna cewa wannan kyauta za ta fito ne daga wani hamshakin ɗan kasuwa a Nijeriya wanda ke daga cikin masu ɗaukar nauyin tawagar Super Eagles. Kyautar za ta fara aiki ne daga wasan na yau, biyo bayan ƙwazon da tawagar ta nuna a matakin rukuni, inda ta samu nasara a dukkan wasannin da ta buga.
- AFCON 2025: Zan Taimaka Wa Uganda Ta Doke Super Eagles Duk Da Mahaifina Ɗan Nijeriya Ne – Ikpeazu
- Jerin ’Yan Wasan Da Za Taka Wa Super Eagles Leda A Gasar AFCON Ta 2026
Nijeriya ta zura ƙwallaye takwas a wasanni uku da ta buga a rukunin C. Wannan sabon tsarin lada ya ninka kyautar dala 5,000 da ƴan wasan ke samu kan kowace ƙwallo a matakin rukuni, kamar yadda shafin BSNSports.com.ng ya rawaito. Shugaban Hukumar Wasanni ta Ƙasa (NSC), Mallam Shehu Dikko, ya tabbatar da wannan ci gaba yayin ganawa da manema labarai a Rabat ranar Lahadi.
A cewarsa, gwamnatin tarayya da abokan hulɗa sun samar da dukkan tallafin da ya dace domin nasarar tawagar. Ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da Asusun AFCON na “Ko-ta-kwana” tun ranar 14 ga Nuwamba, tare da jaddada cewa kyautar za ta ci gaba da ƙaruwa yayin da Super Eagles ke kara matsawa gaba a gasar har zuwa wasan karshe.