Sin Ta Zurfafa Hadin Gwiwar Kasuwanci Da Abokan Huldar BRI A 2025
[ad_1]
Bayanai daga majalisar habaka cinikayyar kasa da kasa ta kasar Sin sun nuna cewa, kamfanoni da masana’antu na kasar Sin sun zurfafa hadin gwiwa mai alfanu da kasashen da ke cikin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya (BRI) a fannin cinikayya, zuba jari da masana’antu a shekarar 2025.
A cikin shekarar da ta gabata, majalisar ta shirya tafiye-tafiyen wakilan kasuwanci guda 407, ciki har da guda 228 zuwa kasashen da ke cikin shawarar BRI, wanda hakan ya taimaka wajen samar da kyakkyawar hulda ga ‘yan kasuwan kasar Sin.
A shekarar 2025, majalisar ta amince da ayyukan baje kolin kayayyaki 707 a kasashen waje a cikin kasashe 43 na shawarar BRI, wadanda aka gudanar a yankin baje kolin kayayyaki da ya kai fadin murabba’in mita 360,000, kuma ya samu halartar kamfanoni kusan 26,500.
A cewar majalisar, domin saukake cinikayya, tsarin habaka kasuwanci na kasar Sin ya bayar da takardun shaidar asali guda miliyan 4.99 da takardun shaidar kasuwanci 559,600 ga kasashen da ke cikin shawarar BRI a cikin watanni 11 na farkon 2025.
Wang Wenshuai, mai magana da yawun majalisar, ta bayyana cewa, “Za mu ci gaba da shirya tawagar wakilan kasuwancin kasar Sin don ziyartar kasashen shawarar BRI a shekarar 2026.” (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza)
[ad_2]
Source link