Sama Da Kwantainoni 600 Ke Sauka Duk Wata A Defo Din Kano —Mahukunta

[ad_1]

Daga Abubakar Abba

Mahukunta a Defo din ajiye kaya da ke a Tashar kan tundu a jihar Kano, sun sanar da cewa, a yanzu Defon din na tarbar sama da Kwantainoni 600 a duk wata, tun farkon fara gudanar da aiki a Defo din shekaru da dama da suka gabata.

An sanar da hakan ne a taron cika shekaru gona na kafa wajen, wanda ya samu halartar masu ruwa da tsaki a fannin.

  • AFCON: Gabon Ta Soke Hukumar Ƙwallon Ƙafa Ta Ƙasar, Ta Dakatar Da Aubameyang
  • Gwamnan Gombe Ya Kafa Hukumar Kula Da Wutar Lantarki

Har ila yau, an kuma yi dubi kan gudaunmawar da Defon din ya samar a yankin na Arewacin kasar nan.

Babban Jami’I na kasa na Defo-Defo Frederik Klinke, ya bayyana cewa, Defon din ya jima yana gudanar da ayyukansa a, musamman a jihohin Kano, Katsina, Kebbi, Maiduguri, da kuma Sokoto.

Ya kuma nuna jin dadinsa kan samun wannan nasarar, wanda ya kara da cewa, hakan ya nuna cewa, an kafa wani sabon tarihi wanda kuma hakan zai kara taimaka wa wajen gudanar da hada-hadar kasuwanci a tsakanin kasashen Jamhuriyar Nijar da kuma kasar Chadi.

Domin marawa wannan adadin goyon baya, an samar da kayan aiki a Defo din tun lokacin da aka fara gudanar da ayyuka a Defo din a shekarar 2015.

Ayyukan sun hada da samar da kayan aiki na zamia, musamman domin a samar kyakaywan tsarin gudanar da zirga-zirgar Kawantainoni da samar da kayan aiki da sauransu.

A jawabinsa a wajen taron Kwantirolan hukumar Kwastam da ke kula da jihohin Kano da Jigawa Dalhatu Abubakar ya bayyana cewa, wannan hadakar ta kara taimaka wa hukumar, musamman a bangaren kara tarawa gwamnati kudaden shiga

Wasu daga cikin shugabannin alumma da suka halarci taron kamar shugaban karamar hukumar Kumbutso Alhaji Sulaiman Abdullahi, ya sanar da cewa, Defo din ta kara taimaka wa wajen kara samar da ayyukan yi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *