Kotu ta ba da umarnin ƙwace kadarorin Malami 57 na wucin gadi

[ad_1]



Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, ta bayar da umarnin ƙwace kadarori 57 da ake zargin mallakin tsohon Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami ne.

Kadarorin, waɗanda suke a Abuja, Kano, Kebbi da kuma Kaduna, darajarsu ta kai sama da Naira biliyan 213.

Wasu kuma kadarorin ana zargin na matarsa, Asabe Bashir, da ’ya’yansa biyu, Abdulaziz da Abiru-Rahman Malami.

Kadarorin sun haɗa da otal-otal, makarantu, shaguna, ofisoshi, masana’antu, da filaye.

Wasu kadarorin da ke Jihar Kebbi, EFCC ta rufe su, yayin da wasu da ke Abuja da Kano ke ci gaba da aiki kamar yadda aka saba.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya bayar da umarnin ne, bayan EFCC ta ce waɗanda ake zargin na iya mallakr kadarorin ta hanyar da ba ta dace ba.

Kotun ta umarci a wallafa hukuncin a dukkanin jaridu na ƙasa.

Wasu daga cikin kadarorin sun haɗa da manyan otal-otal a Abuja da Kano, gine-ginen jami’a, gidan rediyo, da manyan filaye.

Darajar kuɗin wasu daga cikin waɗannan kadarori ta haura biliyoyin Naira.

Kungiyoyin sa-kai ciki har da CISLAC sun yi maraba da wannan hukunci, inda suka bayyana cewa irin wannan hukunci zai ci gaba da kare ƙimar kotu a idon jama’a.

Sun ce ya kamata a magance cin hanci da rashawa don dawo da amincewar jama’a da rage rashin ladabi.

Daraktan CISLAC, Auwal Musa Rafsanjani, ya ce, “Babu wanda yake sama da doka. Idan wani ya ci zarafin doka, ya kamata a hukunta shi, ba tare da la’akari da muƙaminsa ko jam’iyyar siyasa ba.”

Sai dai Malami ya ƙaryata dukkanin tuhume-tuhume da ake masa.

Kotun ta kuma ba da belin Malami, matarsa, da ɗansa a kan kuɗin Naira miliyan 500 kowanensu.

EFCC na ci gaba da bincike da sanya ido a kan kadarorin Kebbi domin tabbatar da rufe su.

A lokaci guda, wasu daga cikin otal-otal da ake zargin mallakin Malami ne da ke Abuja da Kano suna aiki yadda suka saba.

Mai bai wa Malami shawara kan harkokin yaɗa labarai, ya ce ubangidan nasa zai martaba umarnin kotu.

Ya ce, “Tsohon AGF ya bi umarnin kotu kuma yana da yaƙinin cewa tsarin shari’a zai tabbatar da gaskiyarsa. Ka da a gaskata tuhumar da ake masa s kafafen watsa labarai a matsayin tabbatar da laifi.”

Wani masani a shari’a ya ce, “Wannan shari’a tamkar gwaji ne kan yaƙi da cin hanci a Najeriya. Ƙwace kadarori na wucin gadi ba yana nufin laifi ba ne, amma yana nuna cewa kotu na iya ɗaukar mataki idan akwai hujja.”

Shari’ar Malami  na ci gaba da jan hankalin jama’a.

Shugabannin ƙungiyoyi masu zaman kansu, na ci gaba da kira ga ’yan Najeriya su tallafa wa hukumomin yaƙi da rashawa kamar EFCC domin tabbatar da adalci.

Wani jami’in CISLAC ya ƙara da cewa, “Tausaya wa masu riƙe da madafun iko yana raunana yaƙi da rashawa. Dole ne a hukunta kowa domin tura sako mai kyau ga matasa.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *