Gobarar ta kashe mutum 6 ’yan gida ɗaya a Filato

[ad_1]



Wata gobara da ta tashi da daddare a yankin tsohuwar kasuwar Mangu da ke Ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato ta yi sanadin mutuwar iyalan ​​Malam Sanusi Maifaci shida a yankin.

Iyalan waɗanda abin ya shafa sun ce waɗanda suka rasun suna tsakanin mai watanni 4 zuwa mai shekara 12.

Da yake bayyana lamarin, wani kawun waɗanda abin ya shafa Umar Basbangida Aliyu ya ce gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 2 na tsakar daren ranar Alhamis lokacin da iyalan suke barci, lamarin da ya yi sanadin mutuwar yaran.

Aliyu ya bayyana cewa, mahaifiyar mamatan ta samu mummunan rauni kuma a halin yanzu tana jinya a asibitin Allah Nakowa da ke garin Mangu.

Da yake ƙarin bayani, Aliyu ya ce, “Mahaifiyar da ‘ya’yanta tara suna kallon talabijin har zuwa ƙarfe 11 na dare, sai mazan uku a cikinsu suka yi barci suka bar uwa da ’ya’yanta shida.

Ya ce “Ba za mu iya bayyana ainihin musabbabin faruwar lamarin ba, amma abin da muka sani shi ne wutar lantarki kafin su kwanta barci, da misalin ƙarfe 2:30 na tsakar dare aka ce mana gobara ta cinye gidan, mahaifiyar ta yi ƙoƙarin fitar da ‘ya’yanta daga ɗaki, amma ta kasa yin hakan, shi ya sa ta samu raunuka ƙone-ƙone,” in ji shi.

A cewar kawun waɗanda suka rasun, Gwamna Caleb Mutfwang da shugaban Ƙaramar hukumar Mangu sun ziyarci iyalan mamatan inda suka buƙaci da su jajanta musu kan lamarin, inda ya ƙara da cewa Gwamnan Jihar ya yi alƙawarin tallafa wa iyalan domin sake gina gidan.

“Gwamnan Jihar da shugaban Ƙaramayr hukumar sun ziyarce mu ne domin jajantawa, muna godiya ga duk waɗanda suka kawo ɗauki ga ‘yan uwa a lokacin da lamarin ya faru, a lokacin da gobarar ta tashi, mun ga ƙauna daga Musulmi da Kirista waɗanda suka ba da gudunmuwa wajen ganin an ceto waɗanda abin ya shafa.” In ji Aliyu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *