Wike Ya Zargi Wasu ‘Yan Siyasar Ribas Da Ziga Fubara, Ya Ce Dole A Girmama Yarjejeniya

[ad_1]

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya zargi wasu jagororin siyasa a Jihar Ribas da ziga Gwamna Siminalayi Fubara.

Da yake jawabi ga magoya bayansa a Ƙaramar Hukumar Ogu/Bolo, Wike ya ce dole ne a girmama yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a gaban Shugaba Bola Tinubu domin kawo ƙarshen rikicin siyasa a jihar.

  • Sakataren APC Ya Buƙaci Murabus Ɗin Wike Saboda “Tsoma Baki” A Harkokin Jam’iyya
  • AFCON 2025: Super Eagles Sun Murƙushe Mozambique Da Ci 4–0

Ya ce Gwamna Fubara bai bi ƙa’idojin yarjejeniyar ba, duk da cewa manyan shugabanni sun sanya hannu a kanta, ciki har da tsohon gwamna Peter Odili, Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, da sauran shugabannin jam’iyyu.

Wike ya soki ‘yan siyasar da suka amince da yarjejeniyar amma daga baya suka fara faɗar akasin haka, yana mai cewa hakan na iya kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ya jaddada cewa Jihar Ribas na da muhimmanci a siyasar yankin Kudu maso Kudu, kuma ya buƙaci shugabanni su riƙa faɗin gaskiya.

Ya kuma tuno da yunƙurin da wasu ɓangarori suka yi a baya na rusa tsarin jam’iyyar PDP a jihar.

Wike ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa naɗa ‘yan asalin Ribas a manyan muƙaman tarayya, yana cewa Shugaban ya cika alƙawuran da ya ɗauka.

Wasu masu jawabi a taron, ciki har da shugaban Ribas Ijaw Peoples Congress, George Sekibo, sun nuna goyon bayansu ga Wike tare da sukar Gwamna Fubara.

Shugabannin yankin Ogu/Bolo ma sun yaba wa Wike bisa ayyukan ci gaba da naɗe-naɗen muƙamai da ya samar musu.

Taron ya samu halartar manyan ‘yan siyasa, sarakunan gargajiya da sauran al’ummar yankin.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *