Arangamar sojoji da ’yan tawaye ta yi ajalin mutum 6 a Chadi

[ad_1]



Aƙalla mutane shida ne suka rasa rayukansu a yayin wata arangama da ta ɓarke tsakanin sojojin ƙasar Chadi da ƙungiyar ’yan tawaye ta MPRD a kudancin ƙasar.

Rundunar sojin Chadi ta ce faɗan ya ɓarke ne da safiyar Talata a garin Korbol da ke yankin Moyen-Chari, inda sojoji uku suka mutu, yayin da wasu goma suka jikkata.

A nasa ɓangaren, shugaban MPRD, Luc Beyam Bebha ya ce ’yan tawayen sun rasa mayaƙa uku, sannan wasu biyu sun jikkata.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa rikicin ya ɓarke ne bayan da dakarun gwamnati suka yi yunƙurin matsowa kusa da sansanonin ’yan tawayen, inda aka yi musu kwanton ɓauna.

Rahotanni sun nuna cewa rundunar sojin na ƙara yawan jami’anta a yankin da ke iyaka da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Ƙungiyar MPRD wadda aka kafa a 2003 da ke neman kifar da tsarin mulki a ƙasar Chadi, ta ce gwamnatin ta ba su wa’adin miƙa wuya tun ranar Lahadi.

Chadi dai na fuskantar hare-haren ’yan tawaye tun shekaru da dama, tun daga mulkin marigayi Idriss Deby zuwa na ɗansa Mahamat Deby, wanda ya karɓi mulki a 2021 sannan ya lashe zaɓen 2024 da ake taƙaddama a kai.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *