Gobara ta tashi a babbar kasuwar Terminus da ke Jos

[ad_1]



Wata gobara da ta tashi a daren Talata a kasuwar Terminus da ke Jos, babban birnin Jihar Filato, ta kone shaguna 25.

’Yan kasuwa sun ce ma’aikatan kashe gobara na gwamnatin tarayya da na jihar Filato sun isa da gaggawa domin dakile gobarar kafin ta bazu zuwa sauran sassan kasuwar.

Sakataren kungiyar ’yan kasuwar, Zakari Sale, ya shaida wa wakilinmu cewa lamarin ya faru tsakanin karfe 8 zuwa 9 na dare, inda ya ce asarar ba ta kai aka wacce aka yi a watannin baya ba a kasuwar.

“Zuwan ma’aikatan kashe gobara a wurin tare da taimakon wasu ’yan kishin ƙasa ya hana gobarar bazuwa da lalata karin dukiya. Bisa bincikenmu, shaguna kusan 25 ne suka ƙone,” in ji sakataren.

A watan Afrilun 2025, wata gobara mai muni ta lalata shaguna sama da 500, inda asarar ta kai fiye da ta Naira biliyan 1, a cewar hukumomin kasuwar.

Kasuwar Terminus na da tarihin gobara mai muni. A watan Fabrairu 2001, gobara ta lalata manyan sassan kasuwar, ta bar ’yan kasuwa da dama cikin matsanancin hali na kudi.

Da take tsokaci a kan lamarin, Hukumar Kasuwar ta tabbatar da faruwar gobarar a wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, inda ta ce binciken farko bai gano ainihin dalilin gobarar ba tukuna.

A cewar hukumar babban kasuwar, jami’an tsaro sun kewaye yankin domin kare dukiyar ’yan kasuwa da kuma tabbatar da tsari kafin zuwan ’yan kasuwa a kasuwar.

Hukumar tare da sauran hukumomin gwamnati masu ruwa da tsaki sun tabbatar wa jama’a cewa bincike kan gobarar yana gudana, kuma za a ɗauki matakan da suka dace domin hana irin wannan faruwa a nan gaba.

Hukumomin sun tabbatar da cewa babu wanda ya rasa rai, kuma tsaron ’yan kasuwa ya kasance cikin koshin lafiya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *