Magauta sun sa NNPCL a gaba – Ojulari

[ad_1]



Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL), Bashir Bayo Ojulari ya ce mutanen da ba sa nufin Najeriya da alheri sun sa kamfanin a gaba saboda sabbin tsare-tsaren da yake kawowa na inganta fannin man fetur a kasar.

Ya bayyana hakan hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin Manyan Ma’aikatan  Bangare Man Fetur da Iskar Gas na Kasa (PENGASSAN) a hedkwatar kwamfanin da ke Abuja.

Ojulari ya ce duk da yake sun san za su iya fuskantar kalubalen, amma ba za su taba bayar da kai bori ya hau ba a yunkurinsu na inganta rayuwar ’yan Najeriya.

“An sa mu a gaba, amma ba za mu taba bayar da kai ga biyan bukatar dan lokaci ba, saboda hakan ba zai haifar wa da Najeriya da mai ido ba.  Mun san ba yadda za a yi ka kawo canji ba tare da kalubale ba,” in ji Ojulari.

Shugaban kamfanin ya bukaci ’yan Najeriya su kara hakuri da sauye-sauyen, inda ya ce bayan wuya dadi na nan tafe ba da jimawa ba.

Tun da farko shugaban kungiyar ta PENGASSAN, Festus Osifo, ya ce ma’aikatan na man fetur sun je hedkwatar kamfanin ne domin su gode masa kan irin gudunmawar da ya bayar a taron kungiyar na bana da aka yi kwanan nan a Abuja.

Ya kuma ce suna jinjina wa shugaban na NNPPCL saboda abin da ya kira gagarumar nasarar da ya samu ya zuwa yanzu a karkashin shugabancinsa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *