Sin Ta Sha Alwashin Zurfafa Amincewa Da Juna Ta Fuskar Siyasa Tsakaninta Da Afirka Ta Kudu

[ad_1]


Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da Afirka ta kudu, wajen zurfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa, da zage-damtse wajen goyon bayan juna, kan batutuwa dake da alaka da manyan moriyarsu, da abubuwan da suke mayar da hankali a kan su.

Li, ya yi tsokacin ne a jiya Juma’a a birnin Johannesburg na Afirka ta kudu, yayin da yake zantawa da shugaban kasar Cyril Ramaphosa, gabanin bude taron G20 karo na 20, wanda zai gudana a yau Asabar da gobe Lahadi. Ya ce Sin ta sha alwashin aiki tare da Afirka ta kudu, wajen karfafa tsare-tsare karkashin dandaloli irin su BRICS da G20.

A nasa tsokaci kuwa, shugaba Ramaphosa cewa ya yi Afirka ta kudu, ta shirya samar da kyakkyawan yanayi na zuba jari da gudanar da hada-hada ga kamfanonin Sin, kuma kasar a shirye take ta yi aiki tare da sauran kasashen Afirka, wajen cin cikakkiyar gajiya daga managartan manufofin kasar Sin na zurfafa hadin gwiwa da kasashen nahiyar Afirka. (Mai fassara: Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *