Yadda Alkur’ani Ya Dace Da Kimiyya Da Fasahar Karni Na 21
[ad_1]
Alhamdulillahi… kamar yadda duk musulmai suka yi imani cewa, littafin Alkur’ani mai girma, wanda ubangiji tabaraka wata’ala ya saukarwa masoyinsa, kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW, ya zama gagara-badau, don haka, ya gagari duk masana, ta yadda suka gaza kai karshen ilimin da ke tattare acikinsa.
Duk nisan zamani da sauyinsa, za kaga Alkur’ani ya tattaro ilimin wannan zamanin. Don haka, ubangiji ke horo da cewa, “a zurfafa bincike acikinsa”, a wani wuri kuma cewa, “ka ce, ya ubangiji kara min ilimi”.
- Shin Bunkasar Sabbin Fasahohi Na Iya Illata Walwalar Jama’a?
- Ista: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Juma’a Da Litinin A Matsayin Ranakun Hutu
A wannan makon, shafin namu mai albarka, tsakuro mana wani abu ya yi na ilimi daga Tafsirin bana, wanda yayi daidai da fahimtar wannan karni mai cike da kimiyya da fasaha.
Ga wasu da muka tsakuro muku:
Kasa Na Samun Daukaka Ne Da Mutunta Dukkan Al’umma
Shehu Isma’ila Umar Almadda (Mai Diwani), ya cigaba da bayani akan banbancin garuruwa biyu mabanbanta – Birni da Kauye, inda ya ce, Birni yana samun cigaba sabida tsarinsa na sassauyawa duba da yadda Baƙi ke sauka acikinsa amma Kauye, wata rana nemansa ake a rasa sabida tsarinsa na tsayawa kan tsari daya da kin amsar baki.
Birni, ya kan bayar da ‘yancin cakuduwar al’adu, da tsarin sanya tufafi, inda kowace al’ada za ta saka kayan al’adunta kuma wata al’umma ta koyi wani abu daga cikin al’adun wata al’umma da suke cakude a wurin zama daya.
Har ila yau, Birni yana bayar da ‘yancin yin addini, ‘yancin yare, inda Shehin ya yi kira da cewa, a kula da dora Larabci akan sauran Yarurruka, kowane Yare, zai iya zama yaren addini.
‘Yancin siyasa, ‘yancin kasuwanci, ‘yancin kula da lafiyar tsoffi da kananan yara, duk birni ya tanadi wannan.
Akwai ‘yancin tambaya ta hankali wadda zata kawo cigaba ko fadan ra’ayi, duk a tsarin Birni, inda ya kafa misali da cewa, wasu sunce, “da ba a soki tafiyar sufaye ba, da wasu littattafan da ilimi basu samu ba”, haka zalika gun siyasa, “ba don ‘yancin fadan ra’ayi ba, da sukar gwamnati a inda ta gaza, da wasu cigaban ba a same su ba”, don haka, duk kasar da ta bayar da wadannan ‘yancin, ita ta gasgata Allah, don ta yarda komai ba daya ba ne, Allah shi kadai ne “daya”.
Duk kasar da Allah ya albarkace ta karfin tattalin arziki, da na soji amma maimakon shugabanninta su gode wa Ubangiji, sai suka yi girman kai, suka nuna alfasha, Ubangiji ya yi alkawarin sai ya hallakar da wannan gwamnatin.
Da Ilimi Duk Abinda Ke Boye Ya Fito Fili
Tushen ilimi, shi ne ilimin lissafi. Lissafin gane kowane abu, musamman lissafin saba’ul masani, “euler function”, da “pi number”, kusan da su aka yi nukiliya bomb, da shi aka yi kusan komai. Da wannan lissafi, gaibu ta bayyana a sarari, babu wani abu da yake a boye yanzun, da za a ce babu wanda zai iya saninsa, sai dai Hadarar Allah, itama ya zabi wasu bayin shi, Waliyyai Rabbaniyyina.
Rabbaniyyai, ana nufin bayin Allah, kamar yadda za a ce Kanawi – Dan Kano, Sokotowi – Dan Sokoto. Su, rabbaniyyai, bincike suke yi a hadarar Allah, “Arrahman, fas’al bihi kabira”, “wattabi’i sabila man anaba ilayya”, sun son Ubangiji, sabida bincike akansa. Don haka, babu wani Annabi ko bawan Allah da zai ce, “ku zama bayi na – Kunu Ibadalli”, sai dai yace, “ku zama bayin Allah – Kunu Rabbaniyyina,” ku zama arifai ku san hadarar Allah, sai ku fahimci kaza da kaza.
Kur’ani yazo da bayanai filla-filla, ba wani abu da ya bari a baya, idan mutum ya duba Littafin “Sirril akbar”, zai ga wannan duka filla-filla, domin kur’ani yazo da shi.
Albarkar wannan ilimin lissafin, yau duk gaibu ta zama sarari. Duk abin da shekara 200 da suka shige sunan sa karya, ko kuma a ce, ba zai yiwu ba, yau ya zama gaskiya kuma ya yiwu. Ya zama gaskiya ya yiwu har ma yanzu ba wani abu da zamu ji an ce za’ayi a rika mamakin cewa, kaga ba zai yiwu ba.
Toh don haka, da ilimin Kur’anin nan, danAdam ya san asraran halitta. Cewa ba wanda ya san gaibu, idan jahili ne bashi da ilimin da zai san ta sai ya barwa Allah kayan sa. Bai hana malami yazo ya san ta ba. Malami, ba ana nufin malamin fikihu ba, da duk kan girmamashi, ana nufin Malamai masana asraran halitta, da suka hada da malaman physics, malaman binciken tarihi dake hako kasa, malaman Chemistry da sauransu. Duk wanda ya san falsafa, dole ya san akwai Allah, ko ya sani ko bai sani ba dole ya yadda da Allah, dole ya yi imani da Allah, ko ya ce bai yadda ba, toh ya yadda da wani karfi da yafi karfin halitta.Wadanda suka yi nukiliya sun fi kowa tsoran Allah, sun fi kowa tsoran kansu, sun fi kowa tsoran nukiliya, don haka suke tsawatarwa kada kowa yayi, su kuma su cigaba da yi don acigaba da jin tsoran su.
Toh, ubangiji tabaraka wata’ala da ya fadi gaibu, adali ne, haka kawai ba zai faɗmdi abu ba kuma ya cigaba da boye shi don kar a san wannan abun, ba don hakan ya fade shi ba. Ya kawo danAdam ne don ya san komai, yayi kusa da shi ta ibada, yayi kusa da shi ta ilimi, yayi kusa da shi ta ma’arifa, babu wani abu da ya kange cewa ba za’a san wannan ba.
Mu Fahimci Alkur’ani Da Kyau, Don Mu Iya Zama Da Zamaninmu, Kuma Mu Yi Aiki Da Kayan Zamanin
Yana daga cikin maganganun da babban Shehin Malami na wannan karnin, Mai suna Sheikh Muhammadul Shahnun, wanda ya yi akan Alkur’ani bayan ya shafe kusan shekaru 50 yana bincike kan littafin sannan ya rubuta Tafsirin Alkur’ani akan bincikensa.
Sheikh Shahnun, ya fara bincike ne duba da yadda duniyar Musulunci ke ciki a lokacinsa, wanda yake a lokacin, zamanin rikice-rikicen daular Rasha (Sobiet union) ce, inda yaga cewa, ya dace musulmai su fahimci littafinsu da gaske in ba haka ba, akwai matsala a gaba. Da wannan, Shehu Ibrahim Kaulakh ke fada cikin Diwaninsa, “Ku yi gyara, ku ajiye batun cewa, sai Mahdi ya zo, ya same ku akan kuna daidai, sai ku cigaba da tafiya tare”.
Bugu da kari, Shehu Tijjani (RA) ya fada cewa, “ina kauna ga Ubangiji ya kawo wani Namiji (Malami) da zai rairaye cunkoson abin da Malaman Fikihu su ka cusa cikin addini, ya zo mana da gangariya”.
Da yawa, suna tunanin aiki suke yi wa Shari’ar musulunci amma sun kauce hanya, “la tukaddimu baina yadayillahi wa rasulihi”, sabida ketare haddi.
Almaddah, ya yi karin haske da cewa, Mu fahimci Alkur’ani da kyau, don mu iya zama da zamanin mu lafiya, mu yi aiki da kayan zamanin mu, har ya zama ‘ya’yan kowane zamani da za su zo, za su fahimci Alkur’ani kuma su yi aiki da shi da irin kayan zamaninsu.
Sheikh Shahnun, ya fara rubuta Tafsirin Alkur’ani ne a wuraren shekarar 1990, sannan ya ce, “daga shekarar 2050, kar wanda ya kara amfani da fahimtar dake cikin Tafsirin, a yi amfani da fahimtar sabon zamani”.
[ad_2]
Source link