Babu wanda na cewa zan janyewa takara a 2027 — Atiku
[ad_1]
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya musanta cewa yana son ya janyewa wani takara saboda matashin ɗan takara kafin zaɓen 2027.
A baya dai tsohon mataimakin shugaban Ƙasa Atiku ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takarar shugaban Ƙasa a 2027.
Atiku dai ya fice daga Jam’iyyar PDP bayan ya tsaya takarar Shugaban Ƙasa a zaɓen da ya gabata.
A watan Agusta, Atiku Abubakar da wasu ’yan siyasa na adawa da suka haɗa da: tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, tsohon Gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi da tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi da dai sauransu, sun koma jam’iyyar ADC a matsayin jam’iyyar da za su yi amfani da ita wajen ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a 2027.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Paul Ibe ya fitar Atiku ya ce, “Ya zama dole a fayyace wasu rashin fahimtar wasu kalamai da suka taso daga rahoton wata hira da Atiku Abubakar da wasu sassan kafafen yaɗa labarai suka yi da BBC Hausa.
“Bayan nazartar faifan bidiyo da bayanan hirar – a ainihin Hausa da fassarar Turanci – ya nuna cewa ko kaɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasar bai fito fili ya bayyana ko ya ba da shawara ko ma ya nuna cewa yana da niyyar janyewa ga kowa ba.”
A cewarsa, “Atiku Abubakar a fili ya faɗa cewa matasa, da sauran masu neman takarar shugaban ƙasa, suna da ‘yancin shiga yin takara.”
Ya kuma ƙara jaddada cewa, “idan matashin ɗan takara ya fito ta hanyar nasarar lashe zaɓen fidda gwani, zai goyi bayan wannan ɗan takara ba tare da wani shakku ba.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link