Shawarwari 40 Zuwa Ga Uwargida (1)

[ad_1]

1. Kalmar uwargida ita ce macen farko wanda aka fara aura, duk wacce za ta zo sai dai ta shigo a ta biyu ko a ta uku har ma ta huɗu, amma wannan uwargidan ke ce macen farko.

2. A matsayinki na uwargida ke za ki fara gina tubalin rayuwar aurenki, ke ce za ki fara tsara yadda zaman ku zai kasance tare da mijin naki saboda da yawa matar farko ita ce makarantan farko ga rayuwar namiji.

3. Ki kula da ibada domin shi ne tushen komai, ibada ɗajin tsoron Ubangiji ki san cewa dukkan abin da za ki yi koda a ɓoye ne, idan kin ɓoye wa mijinki lallai baki isa ki ɓoye wa Ubangiji ba.

  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci Matasa Su Riƙa Tantance Sahihancin Labari Kafin Su Yaɗa Shi
  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci Matasa Su Riƙa Tantance Sahihancin Labari Kafin Su Yaɗa Shi

4. Haƙuri da kawaici dole ne ki zama hakan domin zaman rayuwar aure ɓangaren haƙuri shi ne babban jigo a cikin aure, idan ba ki da haƙuri komai zaina faruwa shi ya sa ake son uwargida ki zama mai haƙuri.

5. Ladabi da biyayya matuƙar ba ki da wannan, tsaf mijinki za ki fita daga zuciyar sa, ki sani cewa mijinki shugaba ne a gare ki ki masa ladabi da biyayya, matuƙar abin da ya umurce ki bai kauce wa addini ba.

6. Karki mallaki mijinki ta hanyar sihiri, za ki hallaka kuma ranan gobe ƙiyama wuta ta zama makomar ki.

7. Kar ki je wurin wani boka domin neman biyan buƙata, idan ba ki gane kan mijin ki ba, ki hana idonki barci ki kai wa Ubangiji kukanki cikin dare za ki ga dukkan al’amuran ki sun warware miki.

8. Ki kula da tsaftar cikin gidanki, yaranki, mijinki. Domin tsabta aba ce mai kyau kuma yana daga cikin musulunci, idan kika zama ƙazamar mace kenan wulakanci bibbiyu za ki fuskanta.

9. Iya girki yana daga cikin makamin dake sace zuciyar namiji, idan kika iya girki za ki mallaki mijinki kuma kin wuce raini a wajansa.

10. Iyayen mijinki, ki kula dasu ki basu girmansu, ki kyautata masu koda kin lura da mijinki baida niyyan masu abu, ke kiyi amfani da damar ki ki saka ya masu abu, za ki iya yi musu kyauta daidai ƙarfinki, ki faranta masu koda ba waje ɗaya kuke da su ba, saboda sun gama yi miki komai da suka haifi abin da kika aura.

11. Ki iya zauna da dangin mijinki lafiya, idan sun zo wajenki ki kula da su, idan wani abu ya faru ki je masu idan na murna ne ki taya su, idan kuma na baƙin ciki ne shi ma ki taya su ki zauna da su lafiya.

12. Kar ki zama wata ballagazar mace mara sanin mutuncin kanta.

13. Duk rintsi ki riƙa kulawa da gyaran jikinki ba wai ko wane irin takarkace za ki yi amfani da shi wurin gyaran jiki ba, idan ba ki kula ba da hakan sai ya zamar miki matsala a nan gaba, ki sani kar ki bari mijinki ji wani wari a jikinki, ki kula ta wannan ɓangaren da kyau. 14. Ki zama mace da ta iya ado da kwalliya.

15. Duk bayan sati biyu ko kwana goma ki je kitso mai kyau, ki lura da abin da mijinki ya fi so, wani na son ganin matarsa da kitso, wani kuma ya fi son ganin gashin ta haka a gyare.

16. Kar ki zama mai mummunan lafuza ga mijinki, uwargida ki san irin lafuzan da za yi amfani da shi wurin magana da mijinki. 17. Ko ki san cewa uwargida maza suna son macen da ta iya kalamai mai daɗi?

Saboda haka kema ki iya idan ma ba ki iya ba, ki koya ga zamanin Soshiyal midiya. Musamman guruf ɗin mata ana wayar da kai ki tambaya za a koya miki.

Za mu Ci Gaba Mako Mai Zuwa Idan Allah Ya Kai Mu

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *