Nazari Kan Dabarun Shuka Mangoro A Zamanance

[ad_1]

Mangoro na ɗaya daga cikin jerin kayan marmari da masu nomansa ke samun kuɗaɗen shiga da shi, inda wasu daga cikinsu ke ƙara samar wa da kawunansu kuɗaɗen shiga ta hanyar fitar da shi kasuwanni ƙetare.

A nan, wannan nazari zai mayar da hankali ne kan dabarun shuka shi a zamanance, inda za mu zayyano dabarun kamar haka:

Sanin Nau’in Da Ya Kamata Ka Shuka: Kafin ka shuka Mangoro, yana da kyau ka san irin nau’in mangoron da ya kamata ka shuka, domin wasu nau’ikan Mangoron kamar na Alphonso da Lippens, ana da buƙatar su sosai.

  • Yadda Ciwon ‘Glacoma’ Ke Haddasa Makanta
  • Masu Safarar Makamai Sun Faɗa Komar Ƴansanda A Kaduna

Wasu nayin kuskure wajen gwaman nau’ukan Mangoro, idan za su yi shukar, maimakon su san nau’i ɗaya da ya dace su noma.

Samar Da Gurin Da Ya Fi Dacewa: Samun guri mai kyau, zai taimaka wa manominsa wajen samar da amfanin da ya dace tare da kuma samun riba mai yawa.

Haka nan, Mangoro na riƙe ruwa a jikinsa da yawa, inda kuma a hankali ruwan ke raguwa.

Gyaran Gona: Ana shuka mangoro ne bayan an gyara gonar da za a shuka shi, kuma manominsa zai iya yin amfani da dukkan tsarin da yake buƙata wajen shuka shi.

Ana shuka shi ne, akasari daga watan Juli zuwa watan Agusta, domin kamar yadda masana suka bayyana, wannan lokacin ne ya fi dacewa a shuka shi.

Kare Shi Daga Ƙwari Da Kamuwa Da Cututtuka: Ƙwari na yi wa Mangoro illa, musamman a loakacin da Mangoron ke kan girma, saboda haka, ana son ka samo maganin kashe ƙwarin da ya dace, musamman domin rage tabka asara.

Yadda ka mayar da hankali wajen ba shi kariyar da ta dace, musaman don ka samu riba mai ɗimbin yawa.

Yi Masa Ban Ruwa: Ganin cewa, Mangoro na da ƙarfi sosai, ana buƙatar ka tabbatar kana yi masa ban ruwa, musamman idan kana nomansa ne don samun riba.

A saboda haka, ana so ka sani cewa, matuƙar za ka shiga fannin noman Mangoro, dole ne ka sa a ranka cewa; ban ruwa na da matuƙar muhimmanci.

Haka nan, ana son idan an yi kamar daga kwana goma zuwa sha biyar, ka fara mayar da hankali wajen yi masa ban ruwa, domin rashin yi masa ban ruwa, ba zai girma yadda ake so ba.

Samar Da Sarari: Idan za ka shuka Mangoro, ana so ka tabbatar da ka samar da sarari, musamman don sanin kamar tushe nawa ne ya kamata ka shuka, domin rashin samar da sararin zai iya shafar girmansa a kan lokaci.

Har ila yau, ba a son ka dinga shuka shi kusa da nesa da nesa da juna, musamman don su samu sukunin shan iska.

Sararin ya banbanta da yadda wasu manomansa suke yi, domin wasu manoman na barin kamar mita goma zuwa sha uku a yayin shukar.

Sai dai, yin sararin a lokacin shuka shi da kakar rani, ana so ya kai daga mita goma zuwa mita goma, saboda tsawon lokacin da zai shafe kafin ya girma.

Amma a lokacin shuka shi da damina, ƙasar noman a lokacin tafi kyau, saboda haka, ana so ka tabbatar sararin ya kai kamar mita sha uku, inda hakan zai taimaka masa wajen fara yin ‘ya’ya kan lokaci.

Zuba Masa Takin Zamani Da Na Gargajiya: Ka tabbatar da cewa, ƙasar noman ta samu wadataccen takin gargajiya ko na zamani kafin ka shuka Mangoron, inda ake so ƙasar noman ta kasance tana ɗauke da sinadaran potash, nitrogen, boron, phosphorus da sauransu, inda kuma hakan na ƙara taimaka wa wajen bai wa Mangoron kariya daga kamuwa daga cututtuka.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *