Ana iya samun ɓullar cutar sanƙarau a jihohi 11 — NiMet




Hukumar binciken yanayi a Nijeriya (NiMet) ta gano jihohi 11 da ke fuskantar barazanar hatsarin kamuwa da cutar sanƙarau mai taɓa lakar baya da kwakwalwa, inda ta yi kira ga mazauna yankunan da su kasance cikin shiri tare da ɗaukar matakan kariya.

A cikin wata shawarwarin kiwon lafiya da hukumar ta fitar ranar Alhamis, ta yi gargaɗin kan  jihohin Sakkwato, Zamfara, Kebbi, Katsina, Kano, Jigawa, Adamawa, Gombe, Bauchi, Yobe, da Borno a halin yanzu suna fuskantar barazanar ɓarkewar cutar.

A cewar NiMet, ciwon sanƙarau wata cuta ce mai tsanani da ke shafar ƙwaƙwalwa da lakar baya, wadda ƙwayar cutar Neisseria meningitis ke haddasawa.

Hukumar ta ce: “Ciwon sanƙarau cuta ce mai tsanani da ke shafar ƙwaƙwalwa da lakar baya, kuma tana yaɗuwa ta hanyar ɗigon ruwan numfashi, musamman a wuraren da mutane suka yi cunkoso ko kuma inda iska ba ta ratsawa yadda ya kamata.”

Hukumar ta yi gargaɗin cewa cutar na iya yin ƙamari cikin sauri kuma ta zama barazana ga rayuwa idan ba a yi maganinta cikin gaggawa ba.

“Cutar na iya yin ƙamari cikin sauri kuma tana iya kashe mutum cikin sa’o’i kaɗan idan ba a yi jinya ba. Sai dai, gano cutar da wuri da kuma amfani da magungunan kashe ƙwayoyin cuta  na inganta damar rayuwa da rage raɗaɗin matsalolin cutar,” in ji NiMet.

Haka kuma, shawarwarin sun bayyana rukunin mutanen da suka fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar:

“Yara da matasa, mutanen da ke zaune a wuraren cunkoso, mutanen da ke rayuwa a wurare masu ƙura da bushewa, da kuma waɗanda garkuwar jikinsu ba ta da ƙarfi su ne suka fi fuskantar haɗari.”

NiMet ta buƙaci mazauna jihohin da abin ya shafa da su sanya ido kan alamun farko na cutar, waɗanda suka haɗa da: zazzaɓi mai zafi farat ɗaya, ciwon kai mai tsanani, ciwon wuya, amai sannan su gaggauta neman taimakon likita idan waɗannan alamun suka bayyana.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *