Jam’iyyar PDP Za Ta Dawo Da Karfin Ta Bayan Babban Taron Kasa – Saraki
[ad_1]
An bayyana cewa, duk da rikice-rikicen cikin gida da ta addabi jam’iyyar PDP a ‘yan shekarun nan da kuma yadda aka samu manyan jami’anta da masu rike da mukaman siyasa da dama da suka sauya sheka zuwa wasu jam’iyyu, jam’iyyar za ta farfado da karfin ta, za kuma ta yi takara a dukkan matakai a zaben da ke tunkaro mu na 2027.
Wannan tabbacin ya fito ne daga bakin tshohon gwamnan Iihar Kwara kuma tsohon shugaban majalisar dattawa ta kasa a majalisa ta 8, Alhaji Abubakar Bukola Sarai a tattaunawarsa da manema labarai a Abuja. Ya ce, tabbas jam’iyyar ta tafka kurakurai da dama a baya amma a halin yanzu “Mun yi karatun ta natsu, za mu hada kanmu domin tabbatar da mun fitar da jam’iyyar daga halin da take ciiki” in ji shi.
- Wata Ƙungiya Ta Mara Wa Ganduje Baya Don Zama Daraktan Kamfen Ɗin Tinubu A 2027
- Ƙungiyar Matasan Jihar Filato Ta Yi Zanga-Zanga Kan Ƙaruwar Rashin Tsaro
Ya kara da cewa, ‘Babban taron da zai fitar da ‘yan majalisar zartarsawar jam’iyyar da za a gudanar a karshen wannan makon shi ne zai kai ga gudanar da babban taron da zai ga fitar da shugabannin jam’iyyar wadanda za su samu karbuwar hukumar zabe ta kasa INEC, haka kuma zai kai ga sahallewa ‘yan jam’iyyar takara a dukkan matakai” in ji shi.
A kan haka ya nemi dukkan ‘yan jam’iyyar da masu yi mata fatan alhairi su kwantar da hankalinsu domin nan gaba kadan ‘PDP za ta dawo cikin hayyacinta”, ya kara da cewa, da yawa daga cikin wadanda suka sauya sheka zuwa wasu juam’iyyu za su yi gaggawar dawowa cikin PDP, ‘Musamman ganin yawancin jam’iyyun da suke rige-rigen komawa suma suna fama da irin nasu matsalolin”.
A saboda haka ya nemi manya da kanana ‘yan jam’iyyar PDP su kai zuciyarsu nesa, “Mu hada kai domin samun nasarar da kowa yake bukata” in ji shi.
Daga nan ya bukaci ‘yan siyasar Nijeriya su sa kishin kasa a gaba, haka kuma ya nemi talakawa suma su ji tsoron Allah wajen tsare gaskiya a duk inda suke.
A halin yanzu dai ana sa ran dukkan bangarorin PDP za su hadu domin gudanar da babban taron jam’iyyar wanda zai kai ga ganin an sanya ta a jerin jam’iyyun da za su yi takara a zabukkan 2027.
[ad_2]
Source link