Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 5 A Sokoto Da Zamfara, Sun Ƙwato Makamai

[ad_1]

Sojojin Sashe na 2 na ‘Operation FANSAN YAMMA’ sun kashe aƙalla ‘yan ta’adda 5 tare da kwato bindigogi AK-47 guda 5 a jihohin Sokoto da Zamfara.

Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, wanda ke rike da mukamin Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Soji ta 8, Sashe na 2 na Operation FANSAN YAMMA, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

  • Hisbah Ta Kama Mutane 21 A Otel A Kano
  • Matar Da Ta Haifi Ƴan Biyar A Kano Ta Rasu Bayan Haihuwa

A cewarsa, sojojin sun kai hare-hare kan maboyar ‘yan ta’adda a jihohin Sokoto, Zamfara da Kebbi domin kare al’umma da kuma kawar da ‘yan ta’adda.

“A Jihar Sokoto, a ranar 25 ga Maris, 2026, sojojin sun yi arangama sau biyu da ‘yan ta’adda a dajin Magonho, inda suka kashe ‘yan bindiga 3 tare da kwato bindigogi AK-47 guda 3 da kuma babura.

“A Jihar Zamfara kuma, a ranar 25 ga Maris, 2026, sojojin sun yi nasarar kai kwanton bauna a hanyar Gada Maya – Makakari, inda suka kashe ‘yan ta’adda 2 tare da tilasta sauran tserewa a firgice. A yayin harin, an kwato bindiga AK-47 guda 1, mujallu guda 3, harsasai 55 masu tsayin 7.62mm, wayoyin hannu guda 2, da babur guda 1.”

Laftanar Kanal Osoba ya ƙara da cewa ‘yan ta’addan, sun yi ƙoƙarin ɗaukar fansa ta hanyar kai hari ƙauyen Kaida a ranar bayan sun zargi mazauna ƙauyen da haɗin kai da jami’an tsaro. Sai dai sojojin sun gaggauta mayar da martani, inda suka sake kashe wani ɗan ta’adda tare da kwato wata bindiga AK-47.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *