Wane Irin Tasiri Ya Kamata Babbar Kasa Ta Samar Wa Duniya?

[ad_1]

Kasar Sin da kasar Najeriya dukkansu manyan kasashe ne. Sai dai wane irin tasiri ya kamata wata babbar kasa ta samar wa duniya?

A zamanin da muke ciki, wasu manyan kasashe na son nuna karfinsu, ta hanyar cin zarafin sauran kasashe. Na san wannan abun da suke yi, galibin mutanen duniya ba za su yarda da shi ba.

Hausawa su kan ce, babba juji ne. Da wannan karin magana ake nufin cewa, ya kamata a bari mai karfi ya dauki karin nauyi. To, wannan tunani ya zama dai-dai da na Sinawa. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba bayyana cewa, ya kamata manyan kasashe su nuna cikakken karamci, da kokarin sauke nauyin dake bisa wuyansu.

Kyan alkawari cikawa. Wani abun da ya faru jiya ya shaida yadda kasar Sin ke kokarin cika alkawarinta. An ce, a birnin Yaounde na kasar Kamaru, an shirya taron tattauna batun “shirin kasar Sin” karo na 14 a karkashin laimar kungiyar ciniki ta duniya (WTO). Inda wannan shiri ya shafi yin amfani da kudin da kasar Sin ta bayar, wajen ba da taimako ga kasashe mafiya fama da koma bayan tattalin arziki, don ganin sun halarci tsarin WTO tare da samun alfanu.

Duk a wajen taron, ministan kasuwancin kasar Sin, Wang Wentao, da babbar daraktar kungiyar WTO Ngozi Okonjo-Iweala, sun sa hannu kan yarjejeniyar sabunta “shirin kasar Sin”. Kana a cewar jami’in na Sin, kasar a ko da yaushe kasar Sin tana goyon bayan kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen dake nahiyar Afirka, don su ci gajiyar tsarin kasuwanci da ya shafi bangarori daban daban, da more damammakin da kasuwannin kasar Sin suke samarwa, ta hanyar fitar da karin kayayyaki zuwa kasar.

Hakika kasar Sin har kullum tana neman ganin ci gaban tattalin arzikin kasashe daban daban na bai daya, kana ta samar da dimbin taimako ga kasashe mafiya fama da koma bayan tattalin arziki, wadanda suka kunshi kasashe 33 dake nahiyar Afirka. Misali, a fannin cinikayya, tun daga ranar 1 ga watan Disamban shekarar 2024, kasar Sin ta aiwatar da manufar yafe dukkan harajin kwastam da ake karba kan kayayyakin da ake shigar da su kasar Sin daga kasashe mafiya fama da koma bayan tattalin arziki. Kafin daga bisani, kasar ta sanar da habaka tasirin manufar zuwa dukkan kasashe 53 dake nahiyar Afirka da suka kulla huldar diflomasiyya da kasar ta Sin, matakin da zai fara aiki a farkon watan Mayun bana.

Ban da haka, kasar Sin ta dauki matakan saukaka wa kasashe mafiya fama da koma bayan tattalin arziki hada-hadar ciniki da Sin, ciki har da yin amfani da dimbin bukukuwan ciniki da Sin take shiryawa, wajen tallar kayayyakin wadannan kasashen ga jama’ar kasar Sin.

Sa’an nan a fannin masana’antu, kasar Sin tana kokarin zuba karin jari a kasashe mafiya fama da koma bayan tattalin arziki. Inda a nahiyar Afirka, ake ganin yadda kamfanonin kasar ta Sin ke bude karin masana’antu a cikin yankunan raya tattalin arziki da ciniki da aka kafa a kasashen Afirka, wadanda suka shafi sarrafa amfanin gona, da kera kayayyakin gida masu amfani da lantarki, da jigilar kayayyaki, da sabon makamashi, da dai sauransu.

Ta wadannan misalai, muna iya ganin sahihancin kasar Sin a fannin ba da taimako ga kasashe mafiya fama da koma bayan tattalin arziki. Sai dai me ya sa kasar ta sha bamban da wasu kasashen dake yammacin duniya a wannan fanni? Me ya sa take kokarin ba da taimako, yayin da wasu kasashe ke neman cin zarafin saura? Dalili shi ne, tun tuni kasar Sin ta sanya burin kafa al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya a duniya, ta yadda za a tabbatar da ci gaban tattalin arzikin dukkan kasashe, da hadin gwiwar al’ummunsu, da wanzar da zaman lafiya a ko ina a duniyarmu. (Bello Wang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *