Sarkin Musulmi ya buƙaci gwamnonin Arewa suke saurarar ƙorafin jama’a
[ad_1]
Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ya shawarci gwamnonin jihohin Arewa 19 su riƙa sauraron masu sukarsu tare da amfani da shawarwarin da ake ba su domin inganta salon mulkinsu.
Ya bayar da wannan shawara ne a ranar Litinin, yayin taron haɗin gwiwar Gwamnonin Arewa da Sarakunan Gargajiya a Kaduna.
Sarkin Musulmi, ya ce bai kamata shugabanni su yi biris da ƙorafin jama’a ba, musamman a wannan lokaci da Arewa ke fama da matsalolin rashin tsaro, talauci da matsin tattalin arziƙi.
A cewarsa, babu wani gwamna ko shugaban ƙasa da zai nemi ƙuri’un jama’a sannan bayan ya hau mulki ya juya musu baya.
Ya nuna damuwa cewa mutane da dama na zargin gwamnonin da rashin yin aiki, alhali suna fuskantar matsin lamba.
Sarkin ya shawarce su da su rika karɓar ƙorafe-ƙorafe masu amfani tare da gyara inda ya dace, domin hakan na taimakawa wajen yanke shawara mai kyau.
Haka kuma, ya yi kira da a ƙara samun haɗin kai a tsakanin gwamnonin, inda ya ce hakan ne zai taimaka wajen inganta Arewa da daidaita ƙasa baki ɗaya.
Sarkin Musulmi ya tabbatar wa gwamnonin cewa sarakunan gargajiya na tare da su, kuma a shirye suke ba su goyon baya a kowane lokaci.
Ya kuma bayar da shawarar cewa ya kamata gwamnoni da sarakunan gargajiya su riƙa gudanar da taruka akai-akai domin tattauna matsaloli da yanke shawara tare.
A ƙarshe, ya ce sarakunan gargajiya za su ci gaba da bayar da gudummawa wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Arewa da Najeriya gaba baki ɗaya.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link