Kimiyya Da Fasaha Na Da Amfani Amma Dalilin Raya Su Ya Fi Su Muhimminci

[ad_1]

A kwanan baya, jaridar Tech Times ta kasar Amurka ta wallafa wani bayani mai taken “Wani abu mai muhimmanci da ya shafi takarar da kasashen Sin da Amurka suke yi ta fuskar fasahar kirkirarriyar basira ta AI”, wanda ya kwatanta yanayin amfani da hidimar fasahar AI a kasashen biyu. Inda aka ce, wani iyali mai matsakaicin karfin tattalin arziki na kasar Amurka ya kan kashe kudin da yawansa ya kai kimanin dala 720 zuwa 1000 wajen amfani da hidimomi na AI a duk shekara, yayin da wani iyalin kasar Sin da yake more hidimar manhajojin AI na kasar Sin iri daya da na kasar Amurka, kusan ba ya bukatar kashe ko kwabo.

Me ya sa aka samu wannan bambanci? Dalili shi ne, a kasar Amurka, kimiyya da fasaha dabaru ne na neman cin riba ga manyan ’yan kasuwa, amma a kasar Sin, ana kallon kimiyya da fasaha a matsayin muhimman kayayyakin more rayuwa, wadanda gwamnati ke kokarin raya su a kokarin kyautata zaman rayuwar jama’a, da inganta ayyuka.

Kamar yadda aka bayyana a cikin makalar da jaridar Tech Times ta wallafa, an ce kasashen Sin da Amurka sun dauki tsari iri 2 a fannin raya kimiyya da fasaha, inda tsarin Amurka ya shafi samar da dimbin riba ga bangaren da ya samu nasara a takarar da aka yi cikin kasuwa, kana a nata bangare, kasar Sin na son ganin fasahohin zamani sun amfani kowa.

Hakika, a matsayina na Basine, na gane ma idona yadda ake amfani da kimiyya da fasaha wajen kyautata zaman rayuwar jama’a a kasarmu. Yanzu a kasar Sin, ana iya amfani da wayar salula wajen gudanar da kusan dukkan ayyuka na yau da kullum, irinsu sayen kaya, da ganin likita, da sayen tikitin jirgi, da dai sauransu. Kana a fannin sufuri, layin dogo na jirgin kasa mai saurin gudu, wanda tsawonsa ya kusan kai kilomita dubu 50 a kasar, ya ba mutum damar tafiya zuwa duk wani wurin kasar da nisansa ya kai kilomita 1000 cikin wasu sa’o’i. Kana a wurare daban daban na kasar Sin, ana iya ganin yadda ake amfani da jirgin sama marar matuki wajen taimakon manoma jigilar amfanin gona, da amfani da fasahar AI wajen gano cutar da aka kamu da ita, da mai da na’urar Robot a matsayin mai ba da taimako a fannin girke-girken abinci.

Ban da haka, a nahiyar Afirka ma, kimiyya da fasaha na kasar Sin suna taka rawar gani ta fuskar inganta zaman rayuwar jama’a. Misali, a Najeriya, wasu kwararru masu ilimin aikin gona na kasar Sin sun kirkiro wani sabon nau’in shinkafa, wanda ya sa yawan shinkafar da a kan girba cikin gonar da fadinta ya kai kadada 1, karuwa daga ton 5.6 zuwa ton 8. Kana a kasar Morocco, tashar samar da wutar lantarki ta makamashin hasken rana da wani kamfanin kasar Sin ya gina tana samar da wutar lantarki mai tsabta ga miliyoyin magidanta. Ban da haka, cibiyar tattara alkaluman labarin kasa ta Sin da Afirka tana samar da hidimar gargadin kare kai daga bala’u ga kasashe 54 dake nahiyar Afirka, yayin da sabon tsarin biyan kudi na zamani da aka gina a tsakanin bangarorin Sin da Afirka ya sa kudin da ake kashewa wajen biyan kudi yayin gudanar da ciniki raguwa da fiye da kaso 30%. Haka zalika, allunan sola kirar kasar Sin suna samar da damar amfani da wutar lantarki ga karin mutane a sassa daban daban na nahiyar Afirka.

Sanin kowa ne, kimiyya da fasaha suna da muhimmanci, sai dai dalilin da ya sa ake neman raya su ya fi su muhimmanci. Ko ya kasance neman samun karin riba, ko kuma niyyar inganta zaman rayuwar jama’a? Zabin da za a yi tsakaninsu zai tabbatar da tasirin kimiyya da fasaha ga dan Adam a nan gaba. Ganin yadda Sin da Afirka suke kokarin hadin gwiwa da juna a wannan fanni, ya sa ni fahimtar cewa, bangarorin 2 sun riga sun yi zabi mai dacewa. (Bello Wang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *