Aisha Buhari Ta Ziyarci Atiku A Saudiyya
[ad_1]
Uwargidan Tsohon Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, ta ziyarci tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, a ƙasar Saudiyya yayin da suke gudanar da ibadar umrah.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Atiku ya ce ya ji daɗin karɓar Hajiya Aisha Buhari, ’yarta Hanan, da sauran ’yan uwansu a Ƙasar Mai Tsarki domin idabar Umrah.
- Kimiyya Da Fasaha Na Da Amfani Amma Dalilin Raya Su Ya Fi Su Muhimminci
- APC Ta Maye Gurbin Uzodimma Da Masari A Matsayin Shugaban Kwamitin Babban Taronta Na Ƙasa
Atiku ya kuma tuno siyasar da ya yi tsakaninsa da marigayi Shugaba Buhari, inda Buhari ya doke shi a zaɓen Shugaban Ƙasa sau da dama.
Duk da haka, ya ce ganawar da ya yi da iyalansa a Saudiyya ta kasance cikin yanayi na mutunta juna da kyakkyawar mu’amala.
“Na ji daɗin karɓar Hajiya Aisha Buhari, matar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ’yarta Hanan da sauran ’yan uwansu da suka ziyarce ni a Saudiyya.”
Ziyarar na zuwa ne yayin da iyalan shugabannin biyu ke gudanar da ibada a ƙasa mai tsarki.
[ad_2]
Source link