Shekaru 50: An gudanar taron addu’a na musamman ga Murtala Muhammed a Kano
[ad_1]
Iyalan marigayi Janar Murtala Ramat Muhammed tare da malamai da manyan baƙi sun gudanar da addu’o’i na musamman ga tsohon Shugaban Ƙasa na mulkin soji, bayan cikarsa shekaru 50 da rasuwa.
Gidauniyar Murtala Muhammed ce ta shirya taron addu’ar a Masallacin Murtala da ke titin Zoo Road a Kano.
An yi karatun Alƙur’ani da addu’o’in neman rahamar Allah ga marigayin.
Babban Limamin masallacin, Sheikh Kabir Badamasi-Dantaura ne, ya jagoranci sallar Juma’a da kuma addu’a ga marigayin.
Da yake jawabi a wajen taron, ɗaya daga cikin ’ya’yansa, Malam Risqua Murtala Ramat, ya ce taron na ba da damar yin nazari kan rayuwar mahaifinsa tare da ƙarfafa ’yan Najeriya su riƙa tuna gudunmawar shugabannin da suka gabata.
“Shekaru 50 bayan rasuwarsa, har yanzu ana tunawa da shi saboda hidimar da ya yi wa ƙasa.
“Yana da muhimmanci matasa su fahimci irin sadaukarwar da aka yi wajen gina Najeriya,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa marigayi Janar Murtala ya yi fice wajen yaƙi da cin hanci da rashawa tare da tsayawa kan gaskiya, adalci da daidaito.
Tsohon Ministan Harkokin Waje, Ambasada Aminu Bashir Wali, ya bayyana marigayin a matsayin shugaba mai tsayayyen ra’ayi wanda ya rayu ta hanyar yi wa ƙasa hidima.
“Bai tara dukiya ba, kuma ya rasu kusan ba shi da komai. Sadaukarwar da ya yi wa ƙasar nan har yanzu babu irinta,” in ji Wali.
Sauran masu jawabi, ciki har da ’yan uwansa da masu bincike, sun ce duk da cewa bai daɗe a kan mulki ba, Janar Murtala Muhammed ya yi manyan ayyuka.
Daga cikinsu har da ƙirƙirar wasu jihohi da fara shirin mayar da babban birnin ƙasa daga Legas zuwa Abuja.
Sun kuma yi kira ga Musulmi su ci gaba da yi masa addu’a tare da riƙo da kyawawan ɗabi’unsa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link