Wang Yi Ya Yi Tsokaci Dangane Da Dalilan Dadaddiyar Al’adar Ziyarar Da Ministocin Harkokin Wajen Sin Ke Fara Yi A Afirka A Duk Shekara
[ad_1]
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana dadadden kawance tsakanin Sin da nahiyar Afirka, da daidaituwar manufofin Sin dangane da Afirka, da goyon bayan juna tsakanin kasashe masu tasowa, a matsayin dalilan da suka sanya kasashen Afirka kasancewa zangon farko a kasashen ketare, da ministocin harkokin wajen kasar Sin ke fara ziyarta duk shekara cikin shekaru 36 a jere.
Wang, wanda memba ne a ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin da yake hadin gwiwar jagorancin taro na 9, na dandalin tattauna muhimman batutuwa da suka shafi Sin da kungiyar tarayyar Afirka ta AU, tare da shugaban hukumar gudanarwar AUn Mahmoud Ali Youssouf, a helkwatar AU dake birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha.
Wang, ya kara da cewa a bana ake bikin cika shekaru 70 da kaddamar da huldar diflomasiyya tsakanin Sin da nahiyar Afirka, kuma a farkon shekara, al’ada ce mai kyau Sin ta fara ziyartar ’yan uwanta na Afirka, kamar dai yadda ya dace duk wani mutum ya kaiwa ’yan uwansa ziyarar maraba da shiga sabuwar shekara.
Ministan harkokin wajen na Sin, ya ce manufofin cikin gida da na waje na Sin, na ci gaba da gudana lami lafiya, kuma suna samarwa duniya tabbaci da take matukar bukata, yayin da wanzuwarsu ta fadada zuwa cudanyar kasar da kasashen Afirka.
Daga nan sai ya jaddada cewa, duk yadda yanayin kasa da kasa da na shiyyoyi ya sauya, har kullum Sin za ta kasance ta farko wajen mika tallafi a duk lokacin da nahiyar Afirka ke cikin bukata, kana ta farko da za ta tsayawa nahiyar a lokacin da take neman abokan hadin gwiwa. (Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link