Yadda Ake Chinise Rice

[ad_1]

Asssalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.

A yau shafin na mu zai koya mana yadda ake dahuwar Chinise Rice:

Abubuwan da ake bukata:

Shinkafa, Kwai, Mai, Albasa, Tafarnuwa, Citta, Nama, Kori, Magi, Gishiri, Karas, Koran Tattasai, Koran wake, Yalon attaruhu, Jan Tattasai.

Yadda ake hadawa:

Da farko za ki samu tukunya sai ki zuba mai kadan ki dora a wuta, sannan ki kawo kwai ki fasa a wani kwano sai ki dan zuba masa Gishiri kadan sannan ki rage wutar ki zuba a cikin wannan tukunyar da kika dora a wuta sai ki yi ta juya shi har sai ya dan soyu, amma zai barbaje ne ba wai zai yi kamar wainar Kwai ba.

Sannan sai ki kwashe shi a wani abu ki ajiye a gefe daya, sai ki kara Mai daidai yadda zai ishe ki yin abincin, sannan ki kawo Albasa wadda dama kin yanka ta ki zuba, ki kawo dakakkiyar Citta tare da dakakkiyar Tafarnuwa ki zuba ki dan soya su sama-sama,

Sannan ki kawo Nikakken namanki ki zuba ki ci gaba da soyawa har sai naman ya fara soyuwa sai ki kawo Magi, Gishiri, Kori, da duk wani abu na kamshi da kike bukata ki zuba ki ci gaba da soyawa har sai Naman ya soyu amma kada ki sa masa ruwa saboda ba a zuba ruwa.

Sai ki kawo Koran wake da yankakken karas da yankakken Koran tattasai da yalon tarihu da yankakken tattasai ki zuba ki ci gaba da soyawa ya soyu sama-sama, sannan ki kawo Shinkafa wadda dama kin dafa ta ki zuba tare da wannan Kwain da kika soya, sai ki ci gaba da juyawa na tsawon minti 6 har sai sun hade gaba daya.  Za ki  iya hada Salad duk irin wanda kike so ki ci da shi. A ci dadi lafiya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *