’Yan bindiga sun kashe Civilian JTF 8 a Zamfara

[ad_1]



Aƙalla mutum takwas ’yan Ƙungiyar tsaro ta Civilian JTF ko ’yan ƙato da gora aka sanar an kashe a ƙauyen Dan Loto da ke Ƙaramar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.

Harin dai na zuwa ne makonni biyu kacal bayan da wasu ’yan bindiga suka kai hari a wani masallaci tare da kashe wasu masallata biyar ciki har da wani Limami a ƙaramar hukumar.

Dan Loto yana cikin yankin Yandoton Daji, unguwar da ’yan bindigar suka kashe masu ibada biyar a ranar 26 ga Satumba, 2025.

Binciken Daily Trust ya nuna cewa, ’yan bindigar sun yi wa ’yan ƙungiyar ta CJTF kwanton ɓauna ne a lokacin da suke amsa kiran da ‘yan bindigar ke yi na tayar da ƙayar baya ga al’ummar garin Dan Loto.

Usman Yusuf Tsafe ya shaida wa Daily Trust cewa an kashe jami’an CJTF ne a lokacin da suke musayar wuta da ’yan bindigar.

“Akwai yuwuwar ’yan binigar sun samu labarin zuwan jami’an CJTF, don haka suka yi musu kwanton ɓauna.

“’Yan bindigar sun kashe su, suka tsere sai dai sun auka wa jami’an CJTF ne, bayan sun kashe biyar daga cikinsu, sai suka koma daji, ba su kai farmaki ga mazauna garin ba,” in ji shi.

Aliyu Danlami, mazaunin unguwar Yandoton Daji, ya ce sun shiga cikin ruɗani sakamakon harin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *