Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 45 A Jihar Katsina

[ad_1]

Dakarun Sojin Nijeriya sun kashe ‘yan bindiga 45 da suka kai hari ƙauyen Alhazawa a Jihar Katsina.

Jami’an gwamnati a jihar sun ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da yamma bayan arangama tsakanin sojoji da ‘yan bindigar.

  • Harin Ƴan Bindiga A Zamfara: Gwamna Lawal Ya Jagoranci Taron Gaggawa Kan Tsaro
  • Shettima Ya Yi Alƙawarin Zafafa  Yaƙi Da Ta’addanci A Arewa-Maso-Gabas

Rahotanni sun ce tun da farko ‘yan bindigar sun fito ne daga Jihar Zamfara, inda suka kai hari ƙauyen Alhazawa da ke ƙaramar hukumar Danmusa a ranar Alhamis domin satar shanu.

Sai dai mazauna ƙauyen sun yi ƙoƙarin kare kansu, inda suka kashe huɗu daga cikin ‘yan bindigar.

Bayan kwana ɗaya, ‘yan bindigar sun sake taruwa domin su kai hari domin ɗaukar fansa kan mazauna ƙauyen.

Amma a hanyarsu ta zuwa ƙauyen sun haɗu da sojoji, wanda aka yi musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu.

Rahotanni sun ce a lokacin arangamar an kashe ‘yan bindiga 45, yayin da sojoji uku su ma suka rasa rayukansu.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *