Kotu za ta yanke hukunci kan belin Malami ranar 7 ga Janairu
[ad_1]
Wata babbar Kotun tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 7 ga watan Janairun 2026 domin yanke hukunci kan buƙatar belin tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN) tare da ɗansa Abdulaziz da ɗaya daga cikin matansa, Asabe da ake zargi da karkatar da kuɗaɗe.
Mai shari’a Emeka Nwite ya tsayar da ranar ne bayan da ya amsa bahasi daga lauyoyin masu karewa da masu gabatar da ƙara a kan lamarin.
Ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare Malami da ɗansa Abdulaziz Malami da kuma Hajiya Asabe Bashir, ma’aikaciyar kamfanin Rahamaniyya Properties Ltd a gidan gyaran hali da ke Kuje, babban birnin tarayya Abuja har zuwa lokacin da aka ɗage zaman.
Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon ƙasa, EFCC, ta yi zargin cewa Malami da ɗansa da Asabe, sun haɗa baki wajen ɓoye haramtattun kadarori a yankunan Abuja da Kebbi da Kano.
Sai dai waɗanda ake tuhumar sun musanta zargin da ake yi musu.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link